Gowon Da Wasu Fitattun Yan Najeriya 5 Da Aka Yi Karyan Sun Mutu
Akalla fitattun yan Najeriya shida ne aka yada jita-jitan cewa sun mutu a dandalin soshiyal midiya a baya-bayan nan.
Na baya-bayan nan a jerin shine tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Yakubu Gowon, wanda aka yi rade-radin cewa ya mutu a ranar Litinin, 9 ga watan Oktoban 2023.
Sai dai kuma, Gowon ya yi watsi da jita-jitan cewa yana nan da ransa kuma ba gaggawan tafiya yake yi ba.
Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, ga jerin fitattun yan Najeriya shida da aka yi karyan cewa sun mutu.
1. Yakubu Gowon
Rade-radin mutuwar tsohon shugaban mulkin soja ya yadu a soshiyal midiya a ranar Litinin, 9 ga watan Oktoba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hadimin Gowon, Adeyeye E. Ajayi, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya yi watsi da jita-jitan cewa tsohon shugaban kasar ya mutu, PM News ta rahoto.
Sanarwar da ya saki a daren ranar Litinin ta ce:
"Gowon na nan da ransa kuma cikin koshin lafiya.
"Janar Gowon baya gaggawa don zuwa ko'ina."
2. Rotimi Akeredolu
Wani dan Najeriya a jerin shine gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu.
Da yake martani kan rade-radin mutuwar, kwamishinan labarai na jihar, Bamidele Ademola-Olateju, ya bukaci jama'a da su yi watsi da irin wannan kanzon kurege.
Ademola-Olateju, ya ce "gwamnan na nan da ransa kuma yana ta kula da harkokin jihar, da kuma aiwatar da ayyukan jihar."
A yanzu, Akeredolu da ke fama da rashin lkafiya ya dawo bakin aikinsa a matsayin gwamnan jihar Ondo.
3. Ibrahim Babaginda
An yada jita-jitan cewa tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya, ya mutu a watan Disambar 2019.
Jita-jitan mutuwar Babangida ya yadu a soshiyal midiya a safiyar 15 ga watan Disambar 2019.
Sai dai kuma, hadimin Babngida a wancan lokacin, Prince Kassim Agegbua, ya karyata rahoton, cewa tsohon shugaban kasar na nan da ransa cikin koshin lafiya.
4. Olu Jacobs
Ba wai yan siyasa kadai bane suke fama da wannan matsala ta yada jita-jitan mutuwarsu a soshiyal midiya.
Fitaccen jarumin fim Olu Jacobs ya tsinci kansa a cikin irin wannan yanayi mai ban takaici fiye da sau daya wanda na baya-baya da aka yi ya kasance a watan Agustan bara.
Yan kwanaki bayan yada jita-jitan, matarsa, Joke Silva ta garzaya shafin soshiyal midiya don karyata rade-radin.
5. Pete Edochie
Wani jarumin Nollywood da aka yi rade-radin ya mutu shine Pete Edochie.
An fara yada jita-jitan ya mutu a 2012 sannan labarin mutuwarsa ya sake bayyana a soshiyal midiya a 2022.
Anyi zargin cewa jarumin mai shekaru 75 ya mutu ne a hatsarin mota a ranar 8 ga watan Yulin 2022.
Daya daga cikin yaran jarumin, Uche Edochie, ya garzaya dandalin Instagram don bayyana cewa mahaifinsu na nan da ransa cikin koshin lafiya.
Ya kuma wallafa hotonsa, Pete Edochie da jikokinsa.
6. Chiwetalu Agu Chiwetalu
Agu ashima jarumin fim ne da ya karyata rade-radin mutuwarsa da ya yadu a ranar 24 ga watan Fabrirun 2020.
Da yake jawabi kan jita-jitan a shafinsa na Instagram, ya rubuta:
"Idan ka ga irin wannan shirmen rubutun a Facebook, don Allah ka yi karar mai shafin."
Saura kiris zuciyata ta buga da na ji rade-radin mutuwar Gowon inji tsohon minista
A gefe guda, mun ji a baya cewa amakon nan kurum aka fara yada wasu jita-jita cewa Yakubu Gowon ya rasu, ya bar duniya ya na mai shekara 88.
Daga baya aka tabbatar da cewa wannan labari bai da tushe, Janar Yakubu Gowon ya tabbatar da cewa ya na nan a raye har yau.
Edwin Clark wanda ya na da alaka mai kyau da tsohon shugaban na Najeriya ya ce jita-jitar ta kusa jefa shi a cikin matsala.
Asali: Legit.ng