Lagos: Rundunar Soji Ta Tono Bama-Bamai a Wurin da Bam Ya Tashi a Ikeja
- Dakarun sojin Najeriya sun gano ƙarin bama-bamai da wurin da ababen fashewa suka tashi a Ikeja shekaru 21 da suka wuce
- Babban hafsan sojojin ƙasa, Laftanar Janar Lagbaja ya kaddamar da atisayen sake tsaftace wurin ranar Talata a jihar Legas
- A watan Janairu, 2002 ne aka sami tashin Bama-Bamai a sansanin soji da ke Ikeja, lamarin da ya halaka aƙalla rayuka 1,100
Ikeja, jihar Legas - Hukumar sojin Najeriya ta ƙara tono ababen fashewa a wurin da Bam ya tashi shekaru 21 da watanni tara da suka gabata a Ikeja, babban birnin jihar Legas.
Hukumar sojin ƙasa ta Najerriya ce ta tabbatar da haka a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta naanhajar X wanda aka fi sani da Twitter a kwanakin baya.
Taƙaitaccen bayani kan abinda ya faru a 2002
Tashin bama-baman wanda ya auku ranar 27 ga watan Janairu, 2002 a sansanin sojoji da ke Ikeja, ana kyautata zaton ya halaka mutane aƙalla 1,100 yayin da wasu sama da 20,000 suka rasa mahallansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan haka tashin Bama-baman ya jikkata dubbannin mutane tare da jefa wasu da dama cikin halin kaƙanikayi.
An ce Bama-bamai da wasu ababen fashewa sun tashi ne bisa kuskure a cikin sashin ajiye makamai na barikin sojoji sama da shekaru 21 da suka wuce.
Fashewar wadda ta yi kara kusan sau bakwai, cikin kwanaki biyu, ta yi sanadin lalata dukiyoyi a yankin da kewaye. Lamarin da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi.
Rundunar soji ta fara aikin tsaftace wurin da abun ya faru
Da yake jawabi a Legas ranar Talata yayin kaddamar da shirin tsaftace wurin, babban Hafsan Sojojin ƙasa (COAS), Laftanar-Janar Tajudeen Lagbaja, ya ce a karshe rundunar ta soma aikin kwashe abinda ya rage.
COAS ya bayyana cewa rundunar soji ta fara jigilar sauran bama-bamai da ababen fashewar da ba su fashe ba a wancan lokacin zuwa daya daga cikin sansanonin ta da ke Ajilete, jihar Ogun.
Ya ce aikin shara da tsaftace wurin na farko da aka yi a shekarar 2002 ya ƙara tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a yankin Ikeja da kewaye.
Sojoji sun ƙara tono bama-bamai a wurin
Lagbaja ya ƙara da cewa sun gano wasu bama-bamai da ba su fashe ba a wurin da ibtila'in ya faru kuma hakan ne ya nuna akwai buƙatar sake tsaftace wurin a yanzu.
"Ina ƙara tabbatar wa yan Najeriya musamman mazauna Legas da Ogun cewa za a gudanar da wannan aiki cikin ƙwarewa da kuma taka tsantsan da bin matakan da ya dace."
Yan Bindiga Sun Halaka Basarake, Sun Yi Awon Gaba da Mutane da Yawa a Niger
A wani rahoton kuma Yan bindiga sun yi ajalin Basarake, sun tattara jama'a sun yi awon gaba da su a ƙauyukan jihar Neja ranar Talata da daddare.
Rahotanani daga mazauna yankin sun nuna cewa maharan sun haɗa harda mata sun yi garkuwa da su, sun sace dabbobi.
Asali: Legit.ng