Ministan Abuja Wike Ya Girkawa Saraki Abinci, Bidiyon Ya Yadu a Soshiyal Midiya

Ministan Abuja Wike Ya Girkawa Saraki Abinci, Bidiyon Ya Yadu a Soshiyal Midiya

  • A karo na biyu, ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya sake baje kolin kwarewarsa a harkar girki
  • Wasu makonni da suka wuce, an gano Wike a ranar hutu yana rangadawa shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Femi Gbajabiamila girki
  • A wannan karon, Wike ya girgiza intanet yayin da aka gano shi a bidiyo yana girkawa tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki abinci

FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya sake nunawa duniya cewa shi mutum ne mai kwarewa a bangarori da dama.

An gano Wike a cikin wani bidiyo da ya yadu yana girkawa tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki abinci.

Wike ya tsantsarawa Saraki girki
Ministan Abuja Wike Ya Girkawa Saraki Abinci, Bidiyon Ya Yadu a Soshiyal Midiya Hoto: @AedanAsika
Asali: Twitter

Hakan na zuwa ne yan makonni bayan an ga Wike yana girkawa tsohon dan majalisa kuma tsohon kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila abinci.

Kara karanta wannan

Hotunan Wike a Gidan Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Na Tsagin Atiku, Bayanai Sun Fito

A cikin sabon bidiyon, an gano Wike, sanye da farar riga da wando mai ruwan bula, yana zuba sinadarin dandano na girki a cikin tukunya yana juyawa yayin da Saraki ke tsaye a gefe yana kallo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike ya shiga sahun mutane irin Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun wajen baje kolin girkinsu.

A baya bidiyon Gwamna Adeleke ma ya yadu inda aka gano shi yana nunawa duniya kwarewarsa a harkar girke-girke.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani yayin da Wike ya yi wa Saraki girki

A halin da ake ciki, mutane da dama sun garzaya sashin sharhi don yin martani kan lokacin da Wike ya ware yana girkawa tsohon shugaban majalisar dattawan abinci.

@JaiyeIfeoluwa ya ce:

"Tunda suka yi kokari sakawa Wike guba shi da kansa yake girkawa kansa abinci tun lokacin."

@Adeklinsmann2, ta rubuta:

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Yan Gidan Magajiya Suka Bazama Neman Kwastamomi a Kasuwar Legas

"Wike na girki a kodayaushe, wai matarsa bata bi shi Abuja bane."

@bayuuske ya rubuta:

"Ka yiwa APC girki ka yiwa PDP girki ci a nan ci a can."

Wike ya amince da nadin Barr. Benedict Dauda a matsayin mataimaki na musamman

A wani labarin kuma, Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja, ya amince da naɗin Barr. Benedict Daudu a matsayin babban mataimaki na musamman kan harkokin shari'a da hadin gwiwa tsakanin ɓangarori da dama.

Hukumar ta FCTA ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta sanya a shafinta na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) a ranar Talata, 10 ga watan Oktoba, inda ta ƙara da cewa naɗin ya yi daidai da amincewa da ƙwarewar Daudu da tsohon gwamnan jihar Rivers na wa'adi biyu ya yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng