Yan Gidan Magajiya Sun Mamaye Shahararriyar Kasuwa, Suna Bibiyar Kwastomomi

Yan Gidan Magajiya Sun Mamaye Shahararriyar Kasuwa, Suna Bibiyar Kwastomomi

  • An shiga tsananin damuwa game da yadda yan gidan magajiya suka mamaye shahararriyar kasuwa a Lagas
  • Rahotanni sun tabbatar da cewar a yanzu wadannan yan matan sun mayar da kasuwar ta zama dandalinsu suna neman kwastamomi
  • Wannan rahoton ya kayyade farsahinsu daga takaitaccen lokaci, kwanan gida da ma na karshen mako

Ikeja, Lagos - A jihar Lagas, komai ma na iya faruwa, kuma ana yi wa jihar Kallon wajen buga-buga da samun tarin dukiya kasancewarta cibiyar kasuwancin Najeriya.

Ko shakka babu jihar Lagas ce ta fi kowa yawan jama'a a Najeriya idan har za a gudanar da kidaya a yanzu haka. Ana daukar birnin Lagas a matsayin inda mutum ke koyon darasin rayuwa.

Yan gidan magajiya sun sauya dabaru a Lagas
“Gajeren Lokaci 15k, Kwanan Gida 30k”: Yan Gidan Magajiya Sun Mamaye Shahararriyar Kasuwa Hoto: Ikeja City Mall/ PIUS UTOMI EKPEI/ Per-Anders Pettersson
Asali: UGC

Wani rahoton Punch ya tabbatar da cewar a yanzu yan gidan magajiya basa tsayuwa a bakin hanya kamar yadda suka saba da daddare, maimakon haka, sun koma yin dafifi a kasuwar Lagas suna neman abokan ciniki.

Kara karanta wannan

Masanan Duniya Sun Taimaki Tinubu da Muhimman Shawarwari da $1 ta Zarce N1000

Wani shararren wajen siye da siyarwa na Ikeja (ICM) ya zama dandalinsu, inda yan mata da ke ganiyar shekaru 20 da 30 suke fakewa a wajen sanye da dangalallun kayansu suna neman maza da za su kwashe su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farashin da mace ke karba idan aka dauke ta

An tattaro cewa yan gidan magajiya a kasuwar na cajin kudi kimanin N15,000 na dan gajeren lokaci, N30,000 tsawon dare da kuma 50,000 na karshen mako daga Juma'a zuwa Lahadi, harda kudin mota zuwa inda kwastoma ke so.

Wata yar gidan magajiya a ICM ta ce:

"N50,000 daga Juma'a zuwa safiyar Lahadi. Za ka biya kudin motata zuwa wajenka."

Hakazalika, akwai a kasuwar Festival Mall da ke karamar hukumar Amuwo Odofin ta jihar Lagas ana samun yan gidan magajiya da ke sintiri a yankin daddare suna neman maza da za su kwashe su.

Kara karanta wannan

Hotunan Wike a Gidan Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Na Tsagin Atiku, Bayanai Sun Fito

Da take koro jawabi kan ayyukan wadannan yan mata a yankin, wata mazauniyar wajen mai suna Precious ta bayyana cewa lamarin ya zama ruwan dare.

"Wasun su ma a cikin mota suke tarawa da maza. Idan ka tambayesu dalilinsu na shiga wannan aiki na rashin da'a, sai su far maka da zagi, suna fada maka ai bai shafeka ba."

Fusatattun matasa sun halaka wani dan achaba kan satar mazakuta a Abuja

A wani labari na daban, wasu fusatattun matasa sun farmaki wani dan achaba mai suna Yahusa, kan zargin sace mazakutar fasinjansa a yankin Nyanya da ke Abuja.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, wani ganau mai suna Ibrahim Musa, ya ce mummunan al'amarin ya afku ne da misalin karfe 5:12 na yammacin ranar Alhamis, 5 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng