Kano: Gwamnatin Abba Ta Sanya Ranar Ɗaura Auren Yan Mata da Zawarawa

Kano: Gwamnatin Abba Ta Sanya Ranar Ɗaura Auren Yan Mata da Zawarawa

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya zaɓi ranar da za a ɗaura auren mutane 1,800 wanda gwamnatinsa ta ɗauki nauyi a jihar Kano
  • Abba Gida-Gida ya kai ziyara hedkwatar hukumar Hisbah domin duba inda aka kwana dangane da shirye-shirywn bikin
  • Sheikh Aminu Daurawa ya ce wannan ƙoƙari da gwamnatin Abba ta yi ya zo a lokacin da ya dace

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa kawo yanzu an kammala dukkan wasu shirye-shiryen gagarumin ɗaura auren nan da ta kudiri aniyar yi a faɗin jihar.

Sakamakon haka gwamnatin ta sanya ranar Jumu'a, 13 ga watan Oktoba, 2023 a matsayin ranar ƙulla auren ma'aurata 1,800 da ta ɗauki nauyi daga sassan ƙananan hukumomi 44.

Gwamna Abba Ƙabir Yusuf ya kai ziyara hukumar Hisbah.
Kano: Gwamnatin Abba Ta Sanya Ranar Ɗaura Auren Yan Mata da Zawarawa Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Ɗaura auren wanda ake kira da 'Auren Zawarawa" ya kunshi samari da 'yan mata da zawarawa maza da mata kuma gwamnatin Kano ke ɗaukar nauyin komai, Dailytrust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan Bindga 67 Sun Baƙunci Lahira Yayin da Jami'ai Suka Ceto Mutane 20 da Aka Yi Garkuwa da Su a Bauchi

Gwamna ya ziyarci hedkwatar Hisbah

Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ne ya sanar da haka yayin da ya kai ziyara hukumar Hisbah domin duba shirye-shiryen da aka yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma nuna jin dadinsa da irin shirye-shiryen da aka yi a kasa kawo yanzu, ya kuma yabawa hukumar Hisbah da ma’aikatar lafiya bisa yadda suka gudanar da ayyukan da aka dora musu.

Gwamnan ya kuma nuna farin cikinsa ganin yadda shirin ya ƙunshi marasa galihu da kuma masu naƙasa.

Abba Gida Gida ya nuna rashin jin dadinsa da rugujewar gine-ginen ofisoshi da ba a kammala ba a hedikwatar Hisbah ta jihar sama da shekaru takwas ba tare da an kammala ba.

“Duk da irin rawar da Hisbah ta taka wajen tabbatar da zaman lafiya, tsaro, magance matsalolin ma’aurata da munanan dabi’u ba ta samu kulawar da ta dace daga gwamnatin da ta gabata ba tsawon shekaru 8."

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Tarayya Da Wasu Manyan Shugabannin Mata Sun Ƙara Ruguza Jam'iyyar PDP a Arewa

"Wannan gwamnati za ta tabbatar da cewa hukumar ta samu dukkan kulawar da ta dace,” inji gwamna Abba.

Wannan aure ya zo a kan lokaci - Daurawa

Da yake jawabi tun da farko, babban kwamandan Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce kokarin gwamnati na daukar nauyin auren ma’aurata 1800 ya zo a kan lokaci.

Daurawa ya kara da cewa babu shakka shirin zai taimaka wa mutane musamman a wannan mawuyacin hali tare da dakile barazanar yawaitar zinace-zinace.

Jami'an Tsaro Sun Halaka Yan Bindiga 67, Sun Ceto Mutane 20 a Jihar Bauchi

A wani rahoton kuma Jami'an tsaron haɗin guiwa sun yi nasarar kashe 'yan bindiga 67, sun ceto mutane sama da 20 da aka yi garkuwa da su a Bauchi.

Gwamna Bala Muhammed ya jinjina wa jami'an tsaron bisa wannan nasara kana ya umarci su kawar da 'yan bindiga baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262