Seyi Tinubu Ya Jawowa Mahaifinsa Suka Saboda Yawo Cikin Jirgin Shugaban Kasa
- Duk da shi ba kowa ba ne a gwamnatin tarayya, Seyi Tinubu ya na yawo a cikin jirgin fadar shugaban Najeriya
- Yadda ake wasa da dukiyar al’umma ya yi sanadiyyar da wasu su ke sukar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu
- Ba wannan ne karon farko da hakan ta faru ba, ana batar da dukiyar al’umma a ayyukan da ba gwamnati ba
Abuja - Seyi Tinubu wanda mahaifinsa ne shugaban Najeriya ya jawo abin magana saboda ya yi amfani da jirgin fadar shugaban kasa.
Premium Times ta ce abin da ya jawo surutun shi ne hawa jirgin gwamnatin domin zuwa kallon wasan polo da aka shirya a garin Kano jiya.
Wadanda su ka ga abin da ya faru, sun shaida Seyi Tinubu da abokansa sun shigo Kano ne cikin jirgin fadar shugaban kasa a ranar Lahadi.
Manya sun tarbo Seyi Tinubu
Ma’aikatan fadar shugaban kasa da wasu jami’an gidan gwamnatin jihar Kano su ka tarbi yaron na Bola Tinubu, hakan ya sake surutun jama’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga filin jirgi sai yaron shugaban na Najeriya ya wuce filin folo na Usman Dantata Polo zagaye da jami’an ‘yan sanda da masu fararen kaya.
Duk da bai rike da mukamin komai, Legit ta lura da yadda jami’an tsaro da-dama su ke gadin Seyi Tinubu a kusan duk inda ya shiga a Najeriya.
Rahoton FIJ ya ce Tinubu mutum ne mai sha’awar wasan Polo, saboda haka ya zama jagoran kungiyar STL a Legas, kuma ya kan buga wasa.
Da aka gama wasan, sai jirgin fadar shugaban kasar ya sake daukar Mista Tinubu daga Kano zuwa Abuja, ya na zama a babban birnin tarayya.
Mutane sun yi tir da Seyi Tinubu
A Yi Gaba a Dawo Baya: Tinubu Ya Dawo fa Shirin Buhari Na 'Tradermoni', Ya Bayyana Kudaden da Za a Samu a Shirin
Ja’afar Ja’afar wanda fitaccen ‘dan jarida ne da ke Turai ya soki wannan lamari, ya ce ana amfani da dukiyar gwamnati a inda bai dace ba.
‘Dan jaridar ya tuna da yadda hakan ta faru a gwamnatin Muhammadu Buhari, diyar shugaban kasa ta je daukar hoto cikin jirgin a Bauchi.
Da yake magana a shafin Twitter, Bello Anka ya soki yadda jami’an tsaro ke aikin kare Seyi Tinubu, ya ce an yi aro ne daga zamanin baya.
Aliyu Abdullahi Mukhtar ya ce amfani da dukiyar gwamnati wajen abin da bai shafi al’umma ba, zai jawo alamar tambaya a kan gwamnati.
Kira ga gwamnatin Tinubu
A wani rahoto, an ji Hon. Robinson Uwak ya fadawa gwamnatin Bola Tinubu ta rabu da salon da ta dauka na barin farashin Dala a kasuwa.
Irin mahaukacin tashin da Dalar ta yi zuwa N1000 daga N460 a farkon shekarar nan ya jawo tsadar kaya, tsohon 'dan majalisar ya ce da sake.
Asali: Legit.ng