"Ka Zama Shugaba, Ba Mai Raba Kan Al'umma Ba", Kungiyar PDP Ta Soki Sheikh Mansur Sokoto

"Ka Zama Shugaba, Ba Mai Raba Kan Al'umma Ba", Kungiyar PDP Ta Soki Sheikh Mansur Sokoto

  • Kungiyar PDP Musulmai ta gargadi Sheikh Mansur Sokoto kan kalamansa na jawo rikicin addini
  • Shugaban kungiyar a jihar Nasarawa, Jaafar Toto ya bayyana kalaman malamin a matsayin abin takaici
  • Ya gargadi ‘yan siyasa a jihar da su guji saka malaman addini a cikin shari’ar don hukunci na gaskiya

Jihar Nasarawa – Kungiyar PDP Musulmai a jihar Nasarawa ta gargadi Sheikh Mansur Sokoto kan kalamansa na ta da tarzoma.

Legit Hausa ta tattaro cewa Mansur Sokoto ya bayyana cewa Musulunci na cikin hatsari idan jihohin Taraba da Nasarawa su ka koma hannun wadanda ba Musulmai ba.

Kungiyar PDP a jihar Nasarawa ta gargadi Sheikh Mansur kan kalamansa kan hukuncin kotu
Kungiyar PDP Ta Tura Gargadi Ga Sheikh Mansur Sokoto. Hoto: Facebook.
Asali: Facebook

Meye Sheikh Mansur ya ce kan Nasarawa?

Malamin na magana ne yayin da aka yanke hukuncin kotu a jihar Nasarawa inda kotu ta bai wa David Ombugadu na jam’iyyar PDP nasara, Daily Nigerian ta tattaro.

Kara karanta wannan

Abokai 5 Sun Mutu Tare a Mummunan Hadari a Hanyar Zuwa Daurin Aure

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ta kuma rusa nasarar da Abdullahi Sule na jam’iyyar APC ya yi a zaben da aka gudanar a watan Maris.

Yayin da ta ke martani a wata ganawa da manema labari, Kungiyar mambobin PDP Musulmai a jihar ta shawarci Sheikh Mansur da ya kasance shugaba ba wai me ta da zaune tsaye ba.

Shugaban kungiyar, Injiniya Jaafar Toto ya ce kokari ne na jawo rikicin addini a jihar da kuma saka shugabannin addini wurin kawo cikas a shari’ar da ake yi da kuma hana yin abin da ya dace.

Wane martani kungiyar PDP ta yi kan Sheikh Mansur?

Ya ce:

“Mu na shawartar mutanen mu da su guji zuwa wurin Sokoto duk lokacin da wata matsala ta tashi.
“Wannan ya jawo matsala musamman ga wadanda ba su fahimci yadda tsarin jihar ta ke ba wurin yin magana a kan ci gaba da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Yanzu aka fara: Sanata ya ce mulkin Tinubu ya dace da Najeriya, ya fadi dalilai

“Mu na magana ne kan kalaman Sheikh Sokoto da kuma ba shi shawara da ya kasance ya na magana kaman shugaba ba mai son jawo yaki ba.”

Toto ya gargadi Sokoto da ya fita daga sha’anin jihar Nasarawa saboda samun zaman lafiya, The Discover Nigeria ta tattaro.

Kungiyar ta gargadi dukkan ‘yan siyasa da ke jihar da su guji saka malaman addini a cikin wannan shari’ar saboda zaman lafiya da samun hukunci ingantacce.

Mansur Sokoto ya yi martani kan shari’ar Taraba da Nasarawa

A wani labarin, Malamin addini a jihar Sokoto, Sheikh Mansur ya ce Musulunci na cikin hatsari idan har jihohin Taraba da Nasarawa su ka koma hannun wadanda ba Musulmai ba.

Mansur Sokoto ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook inda ya ke magana kan hukuncin kotu na zaben jihar Nasarawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.