Mutane 4 Sun Riga Mu Gidan Gaskiya Yayin Da Mummunan Hatsarin Mota Ya Afku A Legas
- An shiga jimami yayin da wata motar bas ta ci karo da babbar mota a kan haryar Legas zuwa Ibadan da safiyar yau din nan
- Lamarin ya faru a yau inda mutane hudu su ka rasa rayukansu yayin da wasu da dama ke karbar magani a asibitin Sagamu da ke Ogun
- Kakakin Hukumar FRSC, Florence Okpe ta ce a yanzu haka an ajiye wadanda su ka mutu a dakin adana gawarwaki na Sagamu da ke jihar Ogun
Jihar Legas – Akalla mutane hudu sun rasa rayukansu yayin da wasu mutum uku su ka ji raunuka a wani hatsarin mota a jihar Legas.
Hatsarin ya afku ne a yau Litinin a jihar kan hanyar Legas zuwa Ibadan inda wata motar bas ta ci karo da babbar mota, Premium Times ta tattaro.
Yaushe hatsarin ya afku a jihar Legas?
Kakakin Hukumar FRSC a jihar Ogun, Florence Okpe ta tabbatar da faruwar lamarin a Abeokuta babban birnin jihar Ogun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Okpe ta ce babbar motar ta gagara tsayawa duk da shigewa karkashin ta da bas din ta yi a yankin Kara da ke babbar hanyar ta Legas zuwa Ibadan.
Ta kara da cewa mutane 21 wanda su ka hada da mata takwas da kuma maza 13 ne hatsarin ya rutsa da su a jihar.
Wane hali yanzu ake ciki kan hatsarin da ya afku?
Florence ta ce a yanzu gawarwakin da hatsarin ya kashe an kwashe su zuwa dakin adana gawarwaki a asibitin Sagamu da ke Ogun yayin da wadanda su ka ji raunuka su ke karbar kulawa a asibiti mafi kusa, cewar Leadership.
Ta ce:
“Gawarwakin su na ajiye a dakunan ajiyar gawa da ke asibitin Sagamu a Ogun yayin da masu raunuka aka kai su asibiti mafi kusa don ba su kulawa.”
Mutane 8 sun rasa rayukansu a hatsarin mota a Ogun
A wani labarin, akalla mutane takwas ne su ka mutu bayan wani mummunan hatsari ya rusa da wasu mutane a kan hanyar Legas zuwa Ibadan.
Rahotanni sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a ranar 6 ga watan Satumba inda wata mota kirar Toyota ta ci karo da babbar mota.
Kakakin Hukumar FRSC a jihar Florence Okpe ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce hatsarin ya faru ne da misalin karfe 11:30 na safe.
Asali: Legit.ng