Abba Gida Gida Ya Amince Da Biyan Kudin Makarantar Dalibai Da Ke Jami'o'in Najeriya Daban-daban
- Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya amince da sakin makudan kudade don biya wa dalibai da ke wasu Jami'o'i
- Gwamnan ya ce ya ware kudaden ne don taimaka musu samun shaidar kammala karatunsu a Jami'o'in
- Abba Kabir ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter inda ya ce gwamnatin baya ta yi watsi da su tsawon shekaru takwas
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ware makudan kudade don taimakawa dalibai samun takardun kammala karatu.
Gwamnan ya ware kudaden ne ga 'yan asalin jihar Kano da ke karatu a jami'o'i daban-daban a fadin Najeriya.
Wasu dalilai Abba Kabir ya biya wa kudin makaranta?
Injiniya Abba Kabir ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a yau Litinin 9 ga watan Oktoba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami'o'in sun hada da Bells da Al-Qalam da kuma Igbenidion da aka tura su karatu a baya.
Gwamnan ya ce wannan zai taimaka musu wurin samun shaidar kammala karatunsu da gwamnatin baya ta yi watsi da su.
Ya ce:
"A wannan safiyar, na ba da umarnin biyan kudin makarantar daliban jihar Kano da aka tura karatu Jami'o'in Bells, Igbenidion da Al-Qalam a baya.
"Wannan zai taimaka musu wajen samun shaidar kammala karatunsu daga Jami’o’in, wanda gwamnatin baya ta gaza biyan su a tsawon shekaru takwas da ta yi."
Wane gata Abba Kabir ke yi wa dalibai?
A makon da ya gabata ne gwamnan ya kuma amince da biyan Naira dubu 20 ga dalibai mata dubu 45 don saukaka musu a karatunsu.
Gwamnan ya sanar da haka ne yayin bikin cikan Najeriya shekaru 63 a ranar Litinin 2 ga watan Oktoba don inganta harkokin ilmi.
Ya ce ya kaddamar da wannan shirin ne don karfafawa iyaye tura 'ya'yansu zuwa makaranta ba tare da wani tarnaki ba
Abba Gida Gida ya raba wa majinyata N20,000 kowannensu
A wani labarin, Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya rabawa mijinyata Naira dubu 20 ga ko wanne saboda tallafa musu.
Gwamnan ya yi wannan kyautar ce yayin wata ziyarar bazata da ya kai asibitin Sunusi.
Abba Kabir ya kai ziyarar ce asibitin wanda na daya daga cikin tsoffin asibitoci da su ka dade a jihar.
Asali: Legit.ng