Kamfanin NNPC Ya Karyata Ba Da Kwangiloli A Boye Ga Wasu ’Yan Arewacin Najeriya
- Kamfanin NNPP, ya karyata jita-jitar cewa ya ba da kwangilolin gyara bututun mai a boye ga wasu a Arewacin Najeriya
- Kamfanin ya ce ya bi dukkan hanyar da ta da ce wurin ba da kwantiragin don tabbatar da gaskiya
- NNPP ya bayyana haka ne a shafin Twitter a jiya Lahadi 8 ga watan Oktoba don fayyace komai
FCT, Abuja – Kamfanin mai na NNPC ya musanta cewa ya ba da wasu manyan kwangiloli ga wasu ‘yan Arewacin Najeriya.
An yi ta yada cewa shugaban kamfanin, Mele Kyari ya ba da wasu kwangiloli na kula da bututun mai a boye na biliyoyin kudade ga wasu masu ruwa da tsaki a harkar mai a Arewacin Najeriya.
Meye NNPC ya ce kan zargin ba da kwangilolin a boye?
Kamfanin ya bayyana aka ne a shafin Twitter a ranar Lahadi 8 ga watan Oktoba inda ya ce an yada hakan ne don bata wa kamfanin suna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NNPC ya kara da cewa kwantiragin kula da bututun mai din an ba da su ne ta hanyar da ya dace da kuma bin gaskiya na dokokin kamfanin.
Ya ce lokacin ba da wadannan kwangiloli na bututun mai an sanar da neman masu karbarsu da kuma bin duk hanyar da ta dace.
Sanarwar ta ce:
“Kamfanin NNPC ya samu labarin yaduwar wani rahoto cewa ya ba da wasu kwantiragin gyara bututun mai a fadin kasar.
“Ya kamata mu ba da bayani kan gaskiyar abin da ya faru don cire shakku a zukatan mutane.
“Mu na tabbatar muku da cewa wannan rahoton ba shi da tushe kuma an kirkire shi ne don bata wa kamfanin suna.”
Wane sanarwa NNPC ya fitar kan kwangilolin?
NNPC ya kara da cewa:
“NNPC na bin duk wani tsari na bin doka don aiwatar da ayyukansa wanda ya hada da ba da kwangiloli da sauransu.
“kwangilolin da ake magana an tallata su ga mutane ma su bukata wanda a karshe aka ba da su bayan bin ka’idoji da doka.
“Babban burinmu shi ne yin gaskiya wurin tabbatar da bututun mai su na aiki yadda ya kamata don saukaka jigilar mai a kasar baki daya.”
Dantata da wasu attajirai sun samu kwangiloli daga NNPC
A wani labarin, shahararrun attajirai a Najeriya guda hudu sun samu manyan kwangiloli daga kamfanin mai na NNPC.
Kamfanonin da aka bai wa kwangilolin sun hada da A. A Rano da Oilserv da Macready da kuma kamfanin mai na MRS.
Asali: Legit.ng