An Gano Take-Taken Tinubu na Daura Yaron Magu Kan Kujerar Shugaban EFCC
- Akwai yiwuwar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yanke shawarar wanda zai zama shugaban hukumar EFCC na kasa
- Wata majiya ta fara kyankyasa cewa ana kokarin dawo da Mista Olanipekun Olukoyede kan ragamar EFCC yanzu
- Shekaru uku da su ka wuce, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Olukoyede daga Hukumar
Abuja - Idan abubuwa sun tafi yadda ake tunani, Mai girma Bola Ahmed Tinubu zai nadawa hukumar EFCC sabon shugaba na kasa.
Wani rahoto da aka samu a Premium Times ya ce shugaban kasa zai nada Olanipekun Olukoyede a kan kujerar shugaban EFCC.
Idan har aka yi hakan, nadin zai jawo surutu ta fuskar cancantar da doka ta bayyana da kuma watakila yankin da shugaban ya fito.
EFCC: Olanipekun Olukoyede zai dawo
Mista Olanipekun Olukoyede wanda asalinsa lauya ne, ya rike kujerar sakataren hukumar na shekaru biyu a lokacin Ibrahim Magu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A shekarar 2020, Muhammadu Buhari ya na kan karagar mulki, ya dakatar da Olukoyede da kuma shi Mista Ibrahim Magu daga ofis.
Tun daga lokacin da aka kori sakataren tare da wasu manyan darektoci na kasa, har yau bai sake komawa bakin-aiki a hukumar EFCC ba.
Alakar Olukoyede da Ibrahim Magu
Kafin zamansa sakatare na hukumar ta EFCC mai yaki da rashin gaskiya, Mr. Olukoyede ne shugaban ma’aikatan ofishin shugaban.
Wata majiya ta shaidawa jaridar shugaban kasa Tinubu ya zabi Olanipekun Olukoyede ya zama sabon shugaban hukumar ta EFCC.
Sanatoci za su tantance shugaban EFCC
Da zarar an gama komai, fadar shugaban kasa za ta aika sunansa zuwa ga ‘yan majalisar dattawa, su ne doka ta ba damar tabbatar da shi.
A lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya aika sunan Magu, Sanatoci ba su tantance shi ba, abin da Bola Tinubu zai guji faruwarsa.
Kafin Abdulrasheed Bawa, an fahimci ana yawan zaben babban jami’in ‘dan sanda ne ya rike hukumar da gwamnati ta kafa a shekarar 2003.
Tinubu ya yi karyar takardu?
Ana da labarin Atiku Abubakar ya hurowa Bola Tinubu wuta a kan batun takardun kammala jami’a wanda hakan zai iya jawo a tsige shi.
Lauyan da ke Chicago ya ce babu inda ke nuna Tinubu ya aikata laifin da ake zargi. A cewar lauyan, ‘Dan takaran ya na bata lokacinsa ne.
Asali: Legit.ng