Jerin Gwamnonin Da Suka Nada Hadimai 100 Zuwa Sama Da 400
Duk da ƙorafe-ƙorafen da ƴan Najeriya ke yi na cewa gwamnati na buƙatar rage kuɗaɗen da take kashewa a kowane mataki, wasu gwamnonin sun yi naɗe-naɗe masu yawa waɗanɗa suka ba ƴan Najeriya mamaki.
Wasu gwamnonin sun naɗa mataimaka na musamman sama da 40 zuwa sama da 400 tun bayan da suka shiga ofis a ranar 29 ga watan Mayu.
Jihar Adamawa
Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya naɗa hadiman yaɗa labarai guda 46, wannan a ciki banda mataimaka na musamman da manyan mataimaka na musamman da kwamishinoni da shugabannin hukumomin gwamnati da na ma’aikata.
Watanni biyu bayan yin wannan naɗin gwamnan ya ƙara amincewa da naɗin hadimai 103.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Neja
A kwanakin baya ne Gwamna Mohammed Umaru Bago ya naɗa mata 131 mataimaka na musamman, lamarin da ya sanya ya sha suka daga mafi yawan al'ummar jihar.
A cewar Daily Trust, gwamnan ya fara bayar da sanarwar naɗa kodinetoci mata guda 41 a harkokin siyasa, kula da lafiyar mata da yara, hulɗar yaɗa labarai, kungiyar tallafawa mata, samar wa mata sana'o'i, hulɗa da al'umma, da mashawartan gidan gwamnati.
Daga bisani gwamna Bago ya ƙara naɗa mata 90 manyan mataimaka na musamman masu irin wannan muƙami.
Kano
Ya zuwa yanzu gwamna Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya naɗa hadimai kusan 406 waɗanda suke aiki da shi.
Daga cikinsu akwai masu ba da rahoto na musamman, manyan masu ba da rahoto na musamman, mataimaka na musamman, manyan mataimaka na musamman da masu ba da shawara na musamman.
Sama da hadiman 400 ba su haɗa da kwamishinoni da daraktocin ma'aikatu da hukumomin gwamnati ba.
Akwa Ibom
A kwanakin baya ne gwamna Umo Emo ya ƙaddamar da mataimaka 368 da suka fito daga kowace shiyya ta jihar domin cimma manufarsa ta 'ARISE'.
Bayan koke-koke daga wasu ƴayan jam'iyyar PDP da suka fusata, gwamnan ya yi alƙawarin ƙarin mukamai 4000 a cikin shirin kula da unguwanni na birane.
Plateau
Kwanan nan Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato ya yi naɗe-naɗe sama da 200 da suka hada da sakataren gwamnatin jihar da kwamishinoni da shugabannin hukumomin gwamnati da na ma'aikatau da masu ba da shawara na musamman.
Kwanan nan Mutfwang na PDP ya samu nasara a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Filato da ke zamanta a Jos, babban birnin jihar.
Jihohin Da Jam'iyyu Suka Ssmu Nasara a Kotu
A wani labarin kuma, jam'iyyun APC, PDP da LP sun samu nasara a kotunan sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnoni.
A cikin hukunci 22 da kotunan suka yanke ya zuwa yanzu jam'iyyar PDP ta yi nasara a guda 11, APC a guda 10 sai LP ta yi nasara a gud ɗaya.
Asali: Legit.ng