“Ina Biyan N1,500 Duk Wata”: Matashi Ya Baje Kolin Gidan Da Yake Haya a Bidiyo

“Ina Biyan N1,500 Duk Wata”: Matashi Ya Baje Kolin Gidan Da Yake Haya a Bidiyo

  • Wani matashi dan Najeriya da ke rayuwa a cikin wani gida mara kyan gani ya ce yana biyan haya N1,500 duk wata daga kudin shigarsa
  • Matashin ya zagaya da masu kallo cikin gidan nasa wanda ke yoyo a sama da kuma wurin da yake amfani da shi a matsayin kicin
  • Yan Najeriya da suka ga cewa an ba shi tallafin N50,000 don taimakawa rayuwarsa sun tambayi ta yadda za su iya hada kudi don ba shi gudunmawa

Wani bawan Allah mai suna @ositapopcorn, wanda ke taimakawa mabukata domin inganta rayuwarsu, ya zanta da wani mutum da ke fama da gwagwarmayar duniya.

Mutumin da ke fama da talauci ya baje kolin rusasshen gidansa kuma ya ce yana biyan kudin haya N1,500 duk wata.

Matashi ya baje kolin rusasshen gidan da yake rayuwa a ciki
“Ina Biyan N1,500 Duk Wata”: Matashi Ya Baje Kolin Gidan Da Yake Haya a Bidiyo Hoto: @ositapopcorn
Asali: TikTok

Matashi na biyan kudin haya N1,500

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Kwararawa Malalacin Mijinta Ruwa Yana Cikin Bacci, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

Wani bangare na rufin gidan ya yanke, sannan hasken rana na shiga cikin dakin ta wurare daban-daban a bidiyon.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matashin na da bandaki da aka yi da kwano yan mita kadan daga gidansa. Mutum ya ce yana samun kudi N10,000 duk wata daga sana'ar icce da yake yi kuma cewa hakan ya fiye masa sata.

Bayan @ositapopcorn ya gama hira da shi, ya bai wa mutumin kyautar kudi N50k. Yan Najeriya sun cika da mamakin wanda ke karbar kudi a hannunsa da sunan na hayar wannan wuri mai matukar datti.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Amos Magadzo ya ce:

"Yanzu na lura cewa Allah ya yi mun ni'ima."

Lady Pearl ya ce:

"Mutumin da ke karbar kudin hayan nan ba zai samu aljannah."

Mr Nice ya ce:

Kara karanta wannan

“Zan Biya Miliyan 1 a Dare Daya”: Matashi Ya Roki Budurwa Kan Ta Kwana Da Shi

"Abun da ya fi karya mun zuciya, wasu mutane sun mallaki gida da ya kai biliyoyin naira kuma babu kowa a ciki."

rahbeeallure ta ce:

"Ba ni da shi da yawa amma ina so na tura masa 2k idan bai yi kadan ba."

Nicemanny_12 ya ce:

"Ya Allah idan na taba dasa ayar tambaya kan ni'imar da ka yi wa rayuwata..don Allah kada ka duba hakan...wasu lokutan bani da wayo...Yanzu na lura da irin ni'imar da nake da shi."

Ginin coci ya rufta da wani Fasto yayin da su ke addu'o'i a jihar Benue

A wani labarin, mun ji cewa wani ginin coci ya hallaka babban Fasto yayin da ya ruguje a kansa a jihar Benue.

Cocin Dunamis wanda ke Mission Ward a cikin birnin Makurdi ya rushe ne a safiyar yau Talata 3 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng