Mutum Miliyan 1 Za Su Rasa Aikinsu Yayin da Shugaba Tinubu Ya Dakatar da N-Power
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da tsarin N-Power da aka yi shekaru bakwai ana yi
- Hakan zai shafi mutane musamman matasa da-dama da ke samun kudin kashewa a karkashin aikin
- Za ayi bincike a kan abubuwan da su ka gudana, babu ranar dawowa da tsarin na N-Power a Najeriya
Abuja - Mutum fiye da miliyan guda za su rasa hanyar samun kudi a karkashin tsarin N-Power da gwamnatin tarayya da dakatar.
Punch ta ce matakin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta dauka zai shafi dinbin matasan da su ke karbar N30, 000 a kowane wata.
Shugaba Muhammadu Buhari ya fito da tsarin domin rage yawan matasan da ke zaman banza.
Za ayi aman miliyoyi daga N-Power
Alkaluman da aka samu daga ma’aikatar jinkai sun nuna zuwa yanzu akwai matasa 1,300, 000 da su ke yi ko su ka amfana da tsarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ‘yan sahun farko akwai mutane 300, 000 sai wasu mutum 510, 000 a sahu na biyu, sannan akwai matasa 490, 000 da ke sahu na uku.
Rahoton ya ce zuwa yanzu ba a san adadin wadanda aka yaye daga karkashin tsarin ba, amma da-dama su na cin moriya har yanzu.
Aikin N-Power ya tsaya cak
Sanarwar da gwamnatin tarayya ta fitar a ranar Asabar ya tabbatar da matasan da su ke samun na-kashewa a tsarin sun koma gidan jiya.
Mafi yawan masu aikin na N-Power su na koyarwa ne a makarantun gwamnati, sai dai gwamnati ta na zargin akwai sakaci a aikin na su.
Ana ganin wasu ma’aikatan ba su aikin da aka ba su, amma N-Power ta na biyansu albashi, wannan ya jawo ake bincike tun ba yau ba.
Hukumar ICPC ta na cikin masu binciken ba daidai ba da ake zargin ana aikatawa a tsarin.
Atiku Abubakar v Bola Tinubu
A bangaren siyasa, an ji labarin yadda Atiku Abubakar ya hurowa Bola Tinubu wuta a kan zargin ya yi karya kan takardun kammala jami’a.
Lauyan da ke kare shugaban Najeriya a birnin Chicago, Wole Afolabi ya ce babu inda ke nuna Bola Ahmed Tinubu ya aikata laifin da ake zargi.
Asali: Legit.ng