Saboda Tsaro: Matashiya Ta Gargadi Yan Mata Da Su Rabu Da Saurayinta Bayan Ya Siya Mota
- Wani bidiyo mai ban dariya da ke nuno wata mata da saurayinta a mota ya yadu a soshiyal midiya
- Matashiyar ta yi magana da kakkausar murya a wayarta, inda ta aika sako kai tsaye ga sauran yan matan da ka iya jin mararin sahibinta
- Ta ce ta kasance tare da shi tun bai da kudin siyan mota, kuma yanzu da ya mallaki daya, ba za ta lamunci wata ta yi mata kutse ba
Wani bidiyo mai ban dariya na wata mata da ke yawon shakatawa a mota tare da saurayinta ya dauka hankalin mutane a soshiyal midiya
Matashiya na ta magana a wayarta da kakkausar murya, tana mai jan hankalin yan mata da ka iya kyallara idonsu a kan masoyinta.
Ta ce ta kasance tare da shi duk rintsi duk wuya, tun kafin ya mallaki kudin da zai iya siyan mota, kuma yanzu da ya cimma mafarkinsa, ba za ta yadda wata ta shiga tsakaninsu ba.
Ta yi gagarumin gargadi gare su da su nisanci sahibinta kuma abokin rayuwarta mai gaskiya da tsoron Allah.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
Youngflow.tt ta ce:
"Wannan sauti na wadanda saurayinsu ke da mota ne."
Precious onome ta rubuta:
"Ba ke ce za ki fada mani abun da zan yi ba."
Mimi asoms:
"Zan yi amfani da wannan sauti nan ba da jimawa ba da da yardar Allah muradin ransa zai cika na yarda da wannan sosai."
Jacob Fejiro:
"Nawa, mun fara lokacin da bai da wadata sosai ana cikin tafiya da ya fara samu, shine ya rabu da ni ya siya mota, sai ya fara daukar yan mata iri-iri."
Bigfaveee:
"Wasu mazan sun cancanci haka amma ina addu'a Allah kada ya hada mu da baragurbi."
Rhynoceros:
"Bari na ja sunan wasu yan mata 2 da za su iya karbe shi daga hannunki."
Matashi ya yi wa budurwa tayin kwana, ya ce zai bata miliyan 1
A wani labari na daban, wata matashiyar budurwa yar Najeriya, Okoli Classic, ta samu sakon imel a kwanan nan daga wani mutum mai suna Lars Eugene.
A cikin sakon nasa, mutumin ya yi magana kai tsaye ba tare da kwana-kwana ba sannan ya bayyana kansa a matsayin mai bibiyar shafin Tunde Ednut.
Asali: Legit.ng