'Ana Kokarin Ruguza Musulunci Ne Kan Hukuncin Zaben Nasarawa', Farfesa Mansur Sokoto

'Ana Kokarin Ruguza Musulunci Ne Kan Hukuncin Zaben Nasarawa', Farfesa Mansur Sokoto

  • Farfesa Mansur Sokoto ya yi martani kan hukuncin kotun zaben da aka yanke a jihohin Nasarawa da Taraba a kwanakin nan
  • Shehin malamin ya nuna damuwarsa da tunanin cewa me zai je ya dawo idan wadannan jihohi su ka koma hannun wadanda ba Musulmi ba
  • A ranar 30 ga watan Satumba aka yanke hukunci a jihar Taraba yayin da a jihar Nasarawa kuma aka yanke a ranar 2 ga watan Oktoba

Jihar Sokoto – Shahararren malamin addinin Musulunci a Najeriya, Farfesa Mansur Sokoto ya yi martani kan hukuncin kotun zabe a jihohin Nasarawa da Taraba.

Shehin malamin ya nuna damuwarsa kan hukuncin da aka yanke inda ya ce wannan barazana ce ga Musulunci.

Mansur Sokoto ya nuna damuwarsa kan hukuncin kotun Taraba da Nasarawa
Farfesa Mansur Sokoto ya yi martani kan hukuncin zaben Taraba da Nasarawa. Hoto: BBC.
Asali: Facebook

Meye Mansur Sokoto ke cewa kan Taraba da Nasarawa?

Malamin ya ce Musulunci na cikin hatsari idan jihohin biyu su ka koma hannun wadanda ba Musulmai ba a yankin Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Mummunan Ibtila'i Ya Laƙume Rayukan Mutum 6 a Babban Titin Kaduna Zuwa Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Mansur ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook a yau Juma’a 6 ga watan Oktoba.

Wallafawar tasa ta jawo martanin mutane da dama inda kowa ke tofa albarkacin bakinsa kan abin da malamin addinin ya ce.

Wane hukunci aka yanke a Taraba da Nasarawa?

A makon da ya gabata ne kotun sauraran kararrakin zabe ta kwace kujerar Gwamna Abdullahi Sule na jam'iyyar APC a jihar Nasarawa.

Kotun ta kuma tabbatar da David Ombugadu na jam’iyyar PDP a ranar 2 ga watan Oktoba a lafia babban birnin jihar Nasarawa.

Har ila yau, kotun sauraran kararrakin zabe a jihar Taraba ta tabbatar da nasarar Gwamna Kefas Agbu na jam’iyyar PDP a matsayin zababben gwamnan jihar.

Kotun ta yi fatali da dan takarar gwamna a jam’iyyar NNPP, Farfesa Sani Yahaya da rashin gamsassun hujjoji.

Kara karanta wannan

An Saida Fetur a Kan N415 a Maimakon N615 da Attajiri Ya Tausayawa Mutanen Kano

Gwamna Abdullahi Sule tuni ya daukaka kara zuwa kotu don kwato kujerarsa da ya ke ganin an kwace ta ba tare da adalci ba.

Kotu ta kwace kujerar Gwamna Sule na jihar Nasarawa

A wani labarin, Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya rasa kujerarsa bayan kotu ta yi hukunci.

Kotun ta kwace kujerar tare da tabbatar da David Ombugadu na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna. 

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.