Kotu Ta Yankewa Wadanda Suka Sace Mike Ozekhome Shekaru 20 a Kurkuku
- Kotu ta yankewa wasu masu garkuwa da mutane biyu da suka sace babban lauyan Najeriya, Mike Ozekhome, hukuncin shekaru 20 a gidan yari
- Hukuncin na zuwa ne shekaru 10 bayan masu laifin sun sace Ozekhome a Iruekpen a hanyarsa ta zuwa Iviukwe a Agenebode, Edo
- Sai dai kuma, Mai shari'a Binta Nyako, ta sallama tare da wanke wasu biyu da ake tuhuma da laifin ta’addanci
FCT, Abuja - An yankewa Kelvin Ezeigbe da Frank Azuekor, biyu daga cikin mutane hudu da ake zargi da garkuwa da Mike Ozekhome, SAN, hukuncin shekaru 20 a gidan yari.
Mai shari'a Binta Nyako ta babbar kotun tarayya, Abuja, ce ta yanke hukuncin a ranar Juma'a, 6 ga watan Oktoba, jaridar The Nation ta rahoto.
Mai shari'a Nyko ta riki cewa hukuncin zai fara aiki ne daga ranar da aka kama su.
Kotu ta wanke wasu mutum biyu
Haka kuma, mai shari'ar ta sallama tare da wanke sauran mutum biyu da ake zargi, Michael Omonigho da Momoh Haruna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An fara gurfanar da wadanda ake zargin ne a gaban mai shari’a Adeniyi Ademola na babbar kotun tarayya, a ranar 9 ga watan Yunin 2014, bisa tuhume-tuhume 13 da suka hada da hada baki, fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma ayyukan ta’addanci.
An dai zargi Kelvin Ezeigbe, Frank Azuekor, Michael Omonigho da Momoh Haruna, da yin garkuwa da Ozekhome a Iruekpen akan hanyarsa ta zuwa Iviukwe a Agenebode, Edo.
An yi zargin cewa sun yi garkuwa da Ozekhome a Iruekpen akan hanyarsa ta zuwa Iviukwe a Agenebode, Edo, a ranar 23 ga Agusta, 2013.
Ozedkhome ya shafe kimanin makonni uku a tsare kafin aka sake shi bayan biyan naira miliyan 28 a matsayin kudin fansarsa.
Sanata Zam: Iyayena na cikin kuncin rayuwa a sansanin 'yan gudun hijira a Benue
A wani labarin, wani Sanata a jihar Benue, Titus Zam ya bayyana cewa iyayensa na cikin kunci a sansanin 'yan gudun hijira a jihar.
Sanatan wanda ke wakiltar Arewa maso Yammacin jihar ya ce hakan ya faru sanadiyyar hare-haren 'yan bindiga a shekarar 2022, Legit ta tattaro.
Asali: Legit.ng