Mummunan Hadarin Mota Ya Lakume Rayukan Mutum 6 a Titin Kaduna-Abuja
- Wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan babban titin Kaduna zuwa Abuka ya yi ajalin mutane ranar Jumu'a
- Kwamandan FRSC reshen jihar Kaduna, Yusuf Nadabo, ya ce hatsarin ya auku ne saboda gudun wuce ƙima da saɓa dokar tuƙi
- Ya jajantawa iyalan mamatan kana ya buƙaci direbobi musamman na motocin haya su ƙara kulawa
Wata motar haya kirar Gulf mai lamba DKA 555 XF ta yi hatsari a kan babban titin Kaduna-Abuja kusa da Sabon Gaya, Kakau, lamarin da ya yi sanadin asarar rayuka shida.
Rahoton Daily Trust ya ce haɗarin ya faru ne da misalin karfe 7 na safiyar ranar Alhamis sa'ilin da direban motar ya gaza sarrafa ta kuma ya ci karo da shingen kankare.
Kwamandan hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Kaduna, Kabir Yusuf Nadabo, ya tabbatar da faruwar haɗarin ga 'yan jarida.
Ya bayyana cewa tuni jami'ai suka kai gawarwakin wadanda suka mutu zuwa ɗakin ajiye gawa na asibitin St. Gerald Catholic dake Kakuri a karamar hukumar Kaduna ta Kudu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Muhimman abubuwan da suka haddasa hatsarin
Kwamandan ya alakanta musabbabin faruwar hatsarin da rashin kulawa, gudun da ya wuce ƙima, da fashewar tayoyi, inda ya bukaci direbobi da su yi taka-tsan-tsan kana su yi tuƙi a tsanake.
Kwamandan ya nuna damuwarsa kan yadda akasarin hadurra a babbar hanyar sun faru ne tsakanin karfe 4 na safe zuwa 6 na safe da kuma tsakanin karfe 8 zuwa 10 na dare.
Yusuf Nadabo ya ce:
“Hukumar FRSC da sauran masu fafutukar kiyaye tituna na ci gaba da gargadin masu ababen hawa a kan saɓa ka'idoji domin gujewa afkuwar irin abin da muka gani a yau Juma’a."
"Gaskiya abin bakin ciki ne. Muna fatan wannan ya zama darasi, tare da jaddada muhimmancin hakuri, musamman kan hanyar Kaduna zuwa Abuja da ake sake ginawa.”
Daga ƙarshe ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a wannan mummunan lamari, wanda za a iya kauce wa faruwarsa.
An Kama Malami da Dillali Kan Zargin Sayar da Filayen Bakin Titi a Abuja
A wani rahoton na daban kuma Jami'an tsaro sun kama Malamin Coci da wani mutum ɗaya bisa zargin damfarar mazauna haramtattun gine-gine a Abuja.
Rahoto ya nuna waɗan da ake zargin sun fara karɓan kuɗaɗe daga mutanen don kare su daga rusau.
Asali: Legit.ng