Mummunan hatsarin mota ya laƙume ɗaliban jihar Bauchi 21 da Malamansu guda 3 a jihar Kano
Kimanin dalibai mutane 24 ne suka rigamu gidan gaskiya a sanadiyyar wani mummunan hatsari daya rutsa dasu akan hanyarsu ta zuwa jihar Kano daga Jihar Bauchi, inji rahoton BBC Hausa.
Majiyar Legit.ng ta ruwairo wannan lamari ya faru ne a ranar Talata 13 ga watan Feburairu, a daidai garin Gaya na jihar Kano, bayan sun taso tun daga garin Misau na jihar Bauchi, domin ziyarar bude idanu a Kano.
KU KARANTA: Wasu muhimman bayanai guda 7 dake tsakanin Fatima Ganduje da saurayinta, Abolaji
Hukumar kare haddura ta kasa reshen jihar Kano, FRSC, ta bakin Kaakakinta, Kabiru Ibrahim Daura ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa hatsarin ya faru ne lokacin da Motar ta yi taho mu gama da wata babbar mota.
Kaakakin yace daga cikin wadanda suka mutu, 13 maza ne, yayin da sauran mutum 10 kuma mata ne, inda yace tuni aka yi musu jana’iza kamar yadda Musulunci ya tanadar, sa’annan mutum 3 sun jikkata, inda a yanzu haka suke samun kulawa wani Asibiti dake garin Kano.
A wani labara kuma, FRSC ta bayyan wani mummunan hadari da ya faru a ranar Litinin 12 ga watan Feburairu a kauyen Lambu na jihar Kano, wanda ya aika da mutane bakwai barzahu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng