Gwamnan Jihar Benue Ya Ce Ba a Biya Kudin Fansa Kafin Sakin Kwamishinansa Da Aka Sace

Gwamnan Jihar Benue Ya Ce Ba a Biya Kudin Fansa Kafin Sakin Kwamishinansa Da Aka Sace

  • Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue ya bayyana cewa ba a biya ko sisi ba kafin sakin kwamishinan watsa labarai na jihar da aka sace
  • Mista Mathew Abo ya shaƙi iskar ƴanci bayan ya kwashe kwanaki 10 a tsare a hannun waɗanda suka sace shi
  • Gwamnan ya yaba wa jami'an bisa namijin ƙoƙarin da suka yi wajen ganin kwamishinan ya samu ƴancinsa

Jihar Benue - Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue ya ce ba a biya kuɗin fansa ba kafin a saki kwamishinansa na watsa labarai, al'adu da yawon buɗe ido, Mista Mathew Abo.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, 5 ga watan Oktoba, mai ɗauke da sa hannun babban sakataren watsa labaran gwamnan, Tersoo Kula.

Kara karanta wannan

Murna Yayin Da Kwamishina A Arewa Ya Shaki Iskar 'Yanci Bayan Sace Shi Da Aka Yi, Iyalansa Sun Yi Bayani

Gwamna Alia ya ce ba a biya kudin fansa ba kafin sakin Abo
Mista Abo ya shafe kwanaki 10 a tsare bayan an sace shi Hoto: Tahav Agerzua, NPF.
Asali: Facebook

Nawa aka biya kafin a saki Mista Abo?

Gwamnan ya bayyana cewa babu kudin fansa ko sisi da aka biya domin ganin an sako kwamishinan cikin ƙoshin lafiya, rahoton The Guardian ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

“Za mu iya tabbatar da cewa kwamishinan watsa labarai, al’adu da yawon buɗe ido, Matthew Abo, ya samu ƴanci. Tuni dai ya koma wajen iyalansa a Sankera da ke karamar hukumar Ukum inda aka yi garkuwa da shi."
"Sakin nasa ya auku ne sakamakon matsin lamban da jami'an tsaro suka yi wa miyagun bisa umarnin gwamna Hyacinth Alia, wanda a baya ya ba su umarnin tabbatar da cewa an sako Abo."

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, masu garkuwa da mutanen na ci gaba da tsare tsohon shugaban ƙaramar hukumar Ukum, Mista Washima Erukaa, da ɗan uwansa wanda ya je a ɓoye domin tattaunawa da su domin su saki Erukaa, amma sai suka tsare shi.

Kara karanta wannan

Kuma Ku Dana: Gwamnan APC Mai Shirin Barin Mulki Ya Sabbin Nade-Nade Masu Muhimmanci

Gwamna Alia ya yabawa jami'an tsaro

Gwamnan ya yabawa jami'an tsaro bisa ƙoƙarin ganin an sako kwamishinan lafiya, sannan ya ɗora musu alhakin tabbatar da ganin an sako sauran waɗanda aka sace.

Ya kuma bukaci jami’an tsaro da su kasance masu nuna rashin tausayi ga masu aikata laifuka tare da tabbatar da cewa ba su da sukunin gudanar da ayyukansu a jihar.

Mista Abo, wanda aka yi garkuwa da shi a ranar 24 ga watan Satumba, ya kwashe kwanaki 10 a tsare kafin ya samu ƴanci.

An Sace Dalibai a FUDMA

A wani labarin kuma, ƴan bindiga sun kai farmaki a jami'ar gwamnatin tarayya da ke Dutsinma (FUDMA) a jihar Katsina.

Ƴan bindigan waɗanda suka farmaki ɗakunan kwanan ɗalibai mata da ke wajen makarantar sun yi awon gaba da ɗalibai guda biyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng