Matashiya Ta Tashi Kan Jama’a a Soshiyal Midiya Da Yanayin Kitsonta Mai Kama Da Kwando

Matashiya Ta Tashi Kan Jama’a a Soshiyal Midiya Da Yanayin Kitsonta Mai Kama Da Kwando

  • Kitson ban mamaki da wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta yi ya dauka hankalin masu amfani da soshiyal midiya da suka kalli bidiyonta
  • A cikin bidiyon da ya yadu, an gano ta da kitso mai kama da lema yayin da take tafiyarta a cikin kasuwa sannan ta shige adaidaita
  • Bidiyon ya haifar da martani daban-daban inda kitson ya bai wa mutane da dama dariya wasu kuma sun ce wacce ta kitsa gashin haka ta yi kokari

Wata matashiyar budurwa ta dauka hankali sosai yayin da ta baje kolin kitsonta wanda yake daya tamkar da dubu.

Kitson wanda ya yi kama da ta daura kwando a ka ya ja hankalin masu tafiya a cikin wata kasuwa.

Matashiya ta yi kitso mai ban mamaki
Matashiya Ta Tashi Kan Jama’a a Soshiyal Midiya Da Yanayin Kitsonta Mai Kama Da Kwando Hoto: @mufasatundeednut/Instagram.
Asali: Instagram

Yan Najeriya sun cika da mamakin ganin kitso wata matashiya

Wasu da suka cika da mamakin ganin irin kitson da matashiyar ta yi, sun dauko wayoyinsu domin yi mata bidiyo kuma tuni faifan ya yadu a dandalin soshiyal midiya.

Kara karanta wannan

Matashi Na Shirin Yin Wuff Da Dattijuwar Baturiya, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nan take bidiyon ya haddasa cece kuce a soshiyal midiya, inda mutane suka dungi tofa albarkacin bakunansu.

Martanin jama'a kan kitson wata matashiya mai kama da kwando

Mutane da dama sun garzaya sashin sharhi don bayyana ra'ayoyinsu tare da sanyawa kitson suna iri-iri.

Yanayin kitson ya bai wa mutane da dama dariya inda suka dungi yin barkwanci da shi.

@chyddo ta ce:

"Kawai a bata na'urar POS din. Dama ta riga ta mallaki lema."

@rarebreed.xo ta ce:

"Irin wannan kitson an yi a gaba."

@chimdindu_01 ta ce:

"Da ace wannan fitacciyar mace ce, mutane ba za su yi mamaki ba maimakon haka kowa zai so ya gwada shi. Kalmar ADO FASAHA ce. Jinjina ga mai kitson."

@vivianglow_ ta ce:

"Wacce ta yi kitson nan tana da fasaha."

@clarindablondeskincare ta ce:

"Wannan fasaha ce tsantsa."

Kara karanta wannan

Wata Uwa Ta Fashe Da Dariya Ba Kakkautawa Bayan Ganin Saurayin Diyarta a Karo Na Farko, Faifan Muryar Ya Yadu

Mai kitso ta yi wa budurwa aski saboda ta ki biyan kudin kitso, an tafka mahawara kan bidiyon

A wani labarin, wata budurwa a ƙasar Afirika ta Kudu ta zama abin magana bayan ta jefa kanta cikin cakwakiya a shagon gyaran gashi.

Lamarin dai ya fara ne lokacin da wani mai amfani da sunan @AdvoBarryRoux ya sanya bidiyon musayar kalamai masu zafi da aka yi a tsakanin mai yin kitso da budurwar da ta je ayi mata kitso.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng