Dole Dalibi Ya Nuna Shaidar Gwajin Kwayoyi Kafin Samun Gurbin Karatu, Shugaban Jami'ar Abuja

Dole Dalibi Ya Nuna Shaidar Gwajin Kwayoyi Kafin Samun Gurbin Karatu, Shugaban Jami'ar Abuja

  • Jami'ar birnin Tarayya za ta fara gwajin kwayoyi kafin bai wa ko wane dalibi gurbin karatu a nan gaba
  • Shugaban Jami'ar, Farfesa Abdul-Rasheed Na' Allah shi ya bayyana haka inda ya ce za su hada kai da Hukumar NDLEA
  • Hukumar Kula da Jami'o'i a Najeriya (NUC) ta amince da karin tsangayoyi 26 ga Jami'ar ta Abuja

FCT, Abuja - Shugaban Jami'ar Abuja, Farfesa Abdul-Rasheed Na' Allah ya ce duk dalibin da ke neman gurbin karatu sai an yi ma sa gwajin kwayoyi.

Farfesa Na' Allah ya ce Jami'ar na bukatar sanin halin dalibai game da kwayoyi don taimaka musu watsar da ita.

Dole a yi dalibai gwajin kwayoyi kafin ba su gurbin karatu, shugaban Jami'ar Abuja
Gwajin Kwayoyi Ya Zama Dole Kafin Samun Gurbin Karatu, Shugaban Jami'ar Abuja. Hoto: The Guardian.
Asali: Facebook

Wace doka aka saka a Jami'ar Abuja kafin samun gurbin karatu?

Farfesan ya bayyana haka ne yayin shirye-shiryen bikin yaye dalibai karo na 27 a ranar Laraba 4 ga watan Oktoba, Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Tarayya Ya Kai Koken 'Yan Arewa, Ya Faɗi Hanyar Kawo Karshen Matsalar Tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce za su hada kai da Hukumar NDLEA don taimakawa dalibai da ke ta'ammali da kwayoyi barinta don kada su addabi jama'a bayan kammala karatu.

Ya ce yayin bikin, Jami'ar za ta yaye dalibai masu digirin digirgir guda 100 sai kuma masu digiri na biyu mutum fiye da 700.

Dalibai nawa za a yaye a Jami'ar Abuja?

Ya kara da cewa akwai kuma dalibai fiye da dubu bakwai da za a yaye su a ranar Asabar yayin bikin da su ka kammala digiri dinsu a Jami'ar.

Na' Allah ya ce a yanzu sun inganta Jami'ar ta dawo ta duniya inda su ke da tsangayun yarukan duniya kamar Faransanci da Japananci da kuma yaren Portugal.

Ya ce Jami'ar ta mai da koyan daya daga cikin yarukan wajibi ga ko wane dalibi kafin kammala digiri, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Da Ke Tuka Baro a Kasuwa Ya Zama Shahararren Farfesa Da Ake Ji Da Shi

Hukumar Kula da Jami'o'in Najeriya (NUC) ta amince da karin tsangayoyi 26 ga Jami'ar don inganta ilimi.

Dole dalibi ya mallaki kamfani kafin kammala digiri, Farfesa Na'Allah

A wani labarin, shugaban Jami'ar Abuja, Farfesa Abdul-Rasheed Na'Allah ya ce dole dalibi ya mallaki kamfani kafin kammala karatu a Jami'ar.

Farfesan ya ce wannan doka ta zama dole don inganta rayuwar matasa bayan kammala karatu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.