An Koma Gidan Jiya, Fetur Ya Fara Wahala, Farashi Ya Kai N650 a Gidajen Mai
- Cire tallafin fetur da gwamnatin tarayya ta yi bai kawo karshen wahalar samun mai a Najeriya ba
- Ana cigaba da samun layi a gidajen mai yayin da mafi yawan jama’a ke korafi kan tsadar fetur din
- Manyan gidaje sun fara boye fetur, hakan ya nuna karancin kaya ko kuwa shirin kara farashin lita
Abuja - Duk da yunkurin cire tallafin man fetur, jama’a su na cigaba da kokawa a game da tsada da kuma wahalar mai a wasu garuruwan.
Binciken Legit ya shaida mana ‘yan kasuwa su na kara farashin litar man fetur ba tare da sanarwar kari daga gwamnatin tarayya ko NNPCL ba.
A garin Zariya, manyan gidajen mai da-dama a rufe su ke a yammacin Laraba. A gidajen da ake saida man kuwa, farashin lita ya zarce N615.
Masu sana'a su na kuka da tsadar fetur
Wani direban Keke Napep ya shaida mana takaicinsu, ya ce ana ta kara masu kudi kadan-kadan, har sun koma sayen lita a kan N650 a yanzu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, ana kara farashi a hankali, ya ce take-take na nuna ana neman maida farashin N700 alhali mutane ba su iya biyan kudi da kyau.
Manyan gidaje kamar Conooil, Matrix da A. A Rano da ke hanyar jami’ar ABU Zariya a rufe su ke, haka zalika wasu gidajen mai na AYM Shafa.
Babu fetur, babu gyaran mota
A gefe guda, kanikawa su na kokawa da tsadar da man fetur ya yi, su na ganin hakan ya jawo raguwar hawa mota da rashin samun gyaran mota.
Wani ma’aikacin gwamnati da ke aiki a garin Damaturu a jihar Yobe, ya fada mana su na sayen lita ne a kan N650, akasin farashin gwamnati.
Amma ko a makon nan, wani ya fada mana ya saye litan fetur a kan N615 a Aliko Oil a Kano, sai dai layi sun fara bayyana duk da kukan tsada.
Sulaiman, wani mazaunin garin Kano ne da ya ce ko an samu gidajen da ake saida litar man fetur a kan N620, ba su dadewa a aiki su ke rufewa.
Tribune ta ce a garin Sokoto, gidajen mai da-dama a rufe su ke, ragowar wadanda su ke a bude su na saida fetur a kan farashin da ya haura N620.
Wasu da ke sana’ar Keke Napep sun fara nuna takaicinsu, su na cewa za su hakura da sana’ar saboda asarar da su ke yi a dalilin tsadar mai.
Gwamnoni su na cin bashi a jihohi
Duk da kudin da ake samu a FAAC ya karu, rahoto ya nuna akwai wasu jihohin da su ke cigaba da lafto bashi domin su biya albashin ma’aikata.
Wasu manyan bankuna su ka taimakawa jihohi da bashin kusan Naira Biliyan 50 a shekarar nan a daidai lokacin da kudin shiga ya yi masu kasa.
Asali: Legit.ng