Atiku Abubakar Ya Yarda Zai Yi Magana, Kila Zai Yi Bankada a Kan Takardun Tinubu

Atiku Abubakar Ya Yarda Zai Yi Magana, Kila Zai Yi Bankada a Kan Takardun Tinubu

  • Bayan kwanaki kusan uku ana surutu kan takardun Bola Tinubu, Atiku Abubakar zai yi jawabi
  • ‘Dan takaran shugabancin Najeriya ya tsaida yau a matsayin ranar da zai yi wa duniya magana
  • Ana sa ran Atiku Abubakar, GCON zai yi karin bayani a kan shari’ar da yake yi da shugaban kasa

Abuja - ‘Dan takaran PDP a zaben shugaban kasa na 2023, Atiku Abubakar ya amince ya yi magana a kan abubuwan da su ke faruwa a Najeriya.

Ana ta maganganu game da ingancin takardar shaidar shugaba Bola Ahmed Tinubu, Vanguard ta ce Atiku Abubakar ya nuna zai yi karin haske.

Duk da ba ayi wani cikakken bayani ba, amma alamu sun nuna abin da Wazirin Adamawa zai yi magana a kai ba zai wuce shari’ar zabe ba.

Kara karanta wannan

Lamari Ya Canza da Jami’ar Amurka Ta Yi Karin Haske Dangane da Takardar Tinubu

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar ya taso Bola Tinubu a gaba Hoto @Atiku
Asali: Twitter

Tinubu: Atiku Abubakar zai bude baki

Kwanan nan Jami’ar jihar Chicago da ke kasar Amurka ta fitar da takardun da za su karfafa karar zaben da Atiku Abubakar yake yi a kotun koli.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk hayaniyar da ake yi, ‘dan takaran shugaban kasar bai ce uffan ba, lauyoyi, hadimai da magoya baya ya bari su na ta maganganu har yau.

"Kyau Tinubu ya sauka" - Kungiyar HURIWA

Ana haka ne rahoto ya zo cewa kungiyar HURIWA mai rubutu domin kare hakkin Bil Adama a Najeriya ta bukaci Bola Ahmed Tinubu ya yi murabus.

HURIWA ta na so alkalan kotun koli su tsige shugaban Najeriya ta hanyar soke takarar da ya tsaya bisa zargin cewa ya yi amfani da takardun bogi.

Daily Trust ta ce tsohon mataimakin shugaban kasar ya fitar da jawabi a yammacin Laraba, ya na gayyatar jama’a zuwa taron manema labarai.

Kara karanta wannan

Tinubu Zai Zama Shugaban Najeriya Na Farko Da Kotun Koli Za Ta Tsige – Hadimin Atiku

Sanarwar gayyatar da Atiku ya fitar

"Ana sanarwa tare da gayyatar ka zuwa taron manema labarai na duniya na ‘dan takaran shugaban kasarmu, Mai girma Atiku Abubakar, GCON, gobe, Alhamis 5 ga watan Oktoba 2023, da rana.
Ba da dadewa ba, za a sanar da ku ainihin lokacin taron. Ku samu ku halarta, mun gode."

- Daga ofishin Atiku Abubakar

Shari'ar Tinubu, Atiku da Obi

Wole Olanipekun ne ya jagoranci lauyoyin da su ka kare Bola Tinubu a shari’ar zaben 2023 tsakaninsa da Atiku Abubakar da Peter Obi a kotu.

Ku na da labari sauran lauyoyin APC sun hada da: Muiz Banire, Ahmed Raji, Akin Olujimi, Yusuf Ali da Lateef Fagbemi wanda ya zama minista.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng