Gwamna Diri Ya Dawo da Ma'aikata 704 da Aka Kora a Manyan Makarantun Jihar Bayelsa
- Gwamna Diri ya maida ma'aikata sama da 700 da aka kora daga manyan makarantun jihar Bayelsa guda uku
- A wata sanarwa da sakataren watsa labaransa ya fitar, Douye Diri ya ce matakin maida su bakin aiki zai fara aiki daga watan Satumba
- Hakan ya biyo bayan miƙa masa rahoton kwamitin da ya kafa domin gudanar da bincike kan abin da ya jawo ƙorar ma'aikatan a 2018
Jihar Bayelsa - Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, ya amince da sake daukar ma’aikatan da aka kora daga manyan makarantun jihar guda uku.
Jaridar Leadership ta tattaro cewa ma'aikatan su 704 an kore su daga aiki ne a shekarar 2018, amma a halin yanzu gwamnan ya amince a maida su bakin aiki.
Ma'aikatan da lamarin ya shafa sun haɗa da 644 a jami'ar Neja Delta, Amassoma, 48 a kwalejin ilimi ta Isaac Jasper Adaka Boro, Sagbama da 12 a kwalejin fasahar lafiya, Otuogidi.
Da yake jawabi yayin da ya karɓi rahoton kwamitin da ya kafa domin bincike kan korar ma'aikatan, Gwamna Diri ya ce ya amince da shawarwarin kwamitin nan take.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shawarwarin sun haɗa da sake ɗaukar mafi akasarin wadanda aka kora bisa la’akari da bukatun makarantun da kuma biyansu basussukan albashi da sauran hakkokinsu.
Yaushe ma'aikatan za su koma bakin aiki?
A wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa, Mista Daniel Alabrah, ya fitar, ta ruwaito gwamnan na cewa maida su bakin aiki zai fara ne daga watan Satumba bisa shawarar kwamitin.
Ya ce saɓanin rade-radin da wasu masu son sanya siyasa a dukkan al'amuran jihar Bayelsa su ke yaɗa wa, gwamnatinsa ta jima tana aiki kan batun ma'aikatan a ɓoye.
Diri ya jaddada kudirinsa na kyautata rayuwar al’ummar Bayelsa, yana mai cewa ba zai taba yin siyasa da rayuwar al’ummar jihar ba, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Gwamnan ya ce:
“Wannan na daya daga cikin ƙalubalen da muka gada kuma a lokacin da muka zo, mun damu matuka game da abin da ya faru. A shekarar 2022, na kafa wani kwamiti da zai duba lamarin."
Abba Gida-Gida Ya Nada Sabbin Shugabanni 10 Na Wasu Hukumomi a Kano
A wani rahoton na daban kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa sabbin shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin Kano guda 10.
Sunayen waɗanda Allah ya bai wa muƙaman na ƙunshe ne a wata.sanarwa da babban sakataren watsa labaran gwamna ya fitar.
Asali: Legit.ng