Gwamnatin Tarayya Za Ta Dawo Da Sanya Takunkumi Don Dakile Cutar Mashako

Gwamnatin Tarayya Za Ta Dawo Da Sanya Takunkumi Don Dakile Cutar Mashako

  • Gwamnatin Tarayya za ta dawo da sanya takunkumi don dakile cutar mashako da ta addabi jihohin Najeriya
  • Shugaban Hukumar Lafiya a Matakin Farko, NPHCDA, Dakta Shuaib Faisal ya ce jihar Kano ce ke kan gaba
  • Ya bayyana jihohin da su ke kan gaba a yaduwar cutar kamar jihar Kano sai Yobe da Katsina da Borno da sauransu

FCT, Abuja – Gwamnatin Tarayya na duba yiyuwar kakaba wa mutane sanya takunkumi don dakile cutar mashako.

Shugaban Hukumar Lafiya Matakin Farko (NPHCDA), Dakta Shuaib Faisal shi ya fadi haka a yau Laraba 4 ga watan Oktoba a Abuja.

Za a fara sanya takunkumi saboda dakile cutar mashako
Gwamnatin A Najeriya Za Ta Dawo da Sanya Takunkumi Kan Cutar Mashako. Hoto: NPHCDA.
Asali: UGC

Meye ma'aikatar lafiya ta ce kan takunkumi don mashako?

Ya ce ma’aikatar lafiya ta bayyana haka ne don rage yaduwar cutar da ake shaka ta numfashi da kuma iska, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Da Ke Tuka Baro a Kasuwa Ya Zama Shahararren Farfesa Da Ake Ji Da Shi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yanzu haka cutar ta yadu a fadin kasar cikin jihohi 19 wanda jihar Kano ke da kaso 86 na masu dauke da cutar.

Cutar mashako ana kamuwa da ita ne ta hanyar shaker iska mai dauke da kwayar cutar kamar yadda cutar Korona ta ke.

Dakta Faisal ya bayyana yadda cutar ke yaduwa a tsakanin mutane kamar Korona inda ya ba da shawarar yin rigakafi na cutar.

Ya kuma ba da shawarar daukar matakan kariya daga cutar da ya hada da sanya takunkumin fuska kamar yadda aka yi a lokacin Korona.

Ya ce:

“Ana kamuwa da cutar ta hanyar da ake kamuwa da Korona wato ta hanyar iska, wanda za a iya rage yaduwarta ta hanyar sanya takunkumi.
“Sannan wanke hannaye da kuma yin nesa da masu dauke da cutar na daga cikin matakan kariya.”

Kara karanta wannan

Nijar Ta Fallasa Kasa 1 Tak Da Ke Kulla Musu Sharri Don Hada Su Fada Da ECOWAS, Ta Bayyana Matakin Gaba

Wasu jihohi ne su ka fi yawan ma su mashako?

Sai dai Dakta ya ce cutar ta fi kama yara ‘yan kasa da shekaru 15 inda ya ce yara fiye da dubu 8 su ka kamu da cutar, cewar Tribune.

Rahotanni sun tabbatar da cewa jihar Kano ce ke kan gaba da ma su dauke da cutar fiye da dubu 7 sai kuma jihar Yobe da mutane 775 da jihar Katsina da mutane 232.

Sauran sun hada da jihar Borno da mutane 118 sai Jigawa da mutum 23 sai Bauchi da mutane 20 da kuma Kaduna da mutane 17.

Mashako ta hallaka yara 30 a Yobe

A wani labarin, cutar mashako ta kashe yara fiye da 30 da jikkata mutane 42 a jihar Yobe.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an killace mutane da dama a asibitin kwararru da ke Potiskum.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.