Dala $1 Ta Harba Zuwa N1000, Tsohon ‘Dan Majalisa Ya Yi Muhimmin Kira ga CBN

Dala $1 Ta Harba Zuwa N1000, Tsohon ‘Dan Majalisa Ya Yi Muhimmin Kira ga CBN

  • Robinson Uwak ya bukaci babban bankin CBN ya dauki mataki a kan sukurkucewar Naira
  • Tsohon ‘dan majalisar ya na ganin lokaci ya yi da za a tokare Naira, a hana Dala tashi a kasuwa
  • A ra’ayin Uwak, dole sai gwamnati da sauran hukumomi sun zauna sun nemo mafitar tattalin arziki

Abuja - Tsohon ‘dan majalisar wakilai, Robinson Uwak, ya yi kira ga babban banki na CBN ya dauki mataki a game da karyewar Naira.

Leadership ta ce ganin yadda darajar Narya ta ke cigaba da sauka, Hon. Robinson Uwak ya bukaci hukumomi su ceto tattalin arziki.

Bankin CBN
Bankin CBN Hoto: @Cenbank
Asali: Twitter

Nawa ake saida Dala a yau?

Ana saida Dala tsakanin N780 zuwa N1000, farashin ya danganta ne daga bankuna zuwa hannun ‘yan kasuwar canji da aka fi sani da BDC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Da Ke Tuka Baro a Kasuwa Ya Zama Shahararren Farfesa Da Ake Ji Da Shi

Bayanan shafin AbokiFx sun nuna a yau ana saida kowace Dalar Amurka tsakanin N995 da N1000.

Masana su na alakanta tashin farashin kaya da tsadar Dala a kasuwa domin Najeriya ta dogara ne da kayan da ake shigo da su daga waje.

Abin da Robinson Uwak ya fadawa CBN

A jawabin da Robinson Uwak ya fitar a makon nan, ya nuna ya kamata bankin CBN ya yi watsi da tsarinsa na kyale darajar Dala a kasuwa.

‘Dan kasuwan ya na ganin sabon salon da aka kawo na barin farashi a hannun kasuwa bai taimaka wajen farfado da tattalin arziki ba.

Uwak ya bada shawarar a dauki matakan da za su jawo a samu kudi a asusun ajiyan kudin wajen Najeriya kuma a rage shigo da kayan waje.

Rahoton ya ce ‘dan siyasar ya na ganin akwai bukatar Najeriya ta kula da kudinta na Naira.

"Kula da kudin gida zai taimaka na matsakaicin lokaci sai kuma a dauki manyan matakai da za su yi aiki bayan lokaci mai tsawo.

Kara karanta wannan

NLC da TUC Sun Fasa Yajin-Aiki, Kungiya Ta Umarci Ma’aikatanta Su Tafi Ofis a Yau

A daina amfani da Dala wajen sayayyan kayan da za ayi amfani da su a gida kuma sai an shawo kan facaka da dukiya a gwamnati.
Sannan sai mun hadu gaba daya mun samar da hanyar da za ta taimakawa tattalin arziki nan gaba.”

- Robinson Uwak

NLC-TUC sun sasanta da gwamnati

A zaman karshe da aka yi, an ji labari Joe Ajaero, Emmanuel Ugboaja, Festus Osifo da Nuhu A. Toro su ka wakilci ‘yan kwadago a Aso Rock.

Daga bangaren gwamnati akwai ministocin tarayya da su ka sa hannu a yarjejeniyar da ta bada dama ma'aikata su ka fasa shiga yajin-aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng