Gwamna Ya Aika Ta’aziyya Yayin da Aka Yi Rashin Dattijo a Arewacin Najeriya
- Gwamnan jihar Jigawa ya sanar da mutuwar tsohon shugaban NSPMC, Alhaji Baffa Suleiman
- Marigayin ya rasu ya na shekara fiye da 80 da haihuwa, shi ne shugaban kungiyar dattawan Jigawa
- A rana daya aka rasa Baffa Suleiman da mashahurin likitan nan da aka yi a tarihi, Umaru Shehu
Jigawa - Labari ya zo cewa daya daga cikin tsofaffin shugabannin kamfanin NSPMC na Najeriya, Baffa Suleiman, ya rasu a makon nan.
Premium Times ta ce Alhaji Baffa Suleiman wanda ya na cikin dattawan da ake da su a Arewacin Najeriya, ya kwanta dama a ranar Talata.
Kafin rasuwarsa, Marigayi Baffa Suleiman shi ne shugaban kungiyar dattawa na jihar Jigawa, kuma ana girmama masa a duk Najeriya.
Baffa Suleiman ya kwanta dama
Mai girma Gwamnan Jigawa, Umar Namadi ya sanar da labarin mutuwar wannan Bawan Allah, ya na mai jimamin irin rashin da aka yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A jawabin da ya fitar, Blueprint ta ce gwamnan ya tabbatar da mutuwar dattijon a safiyar Talata, ya ce an bar gibin da zai yi wahalar ciko.
Ta'aziyyar Gwamnan jihar Jigawa
"Cikin zulumi da jimami na ke sanar da rasuwar babban shugaba kuma katangar al’ummar Jigawa, Sulaiman Baffa, shugaban majalisar dattawa.
Alhaji Sulaiman Baffa ya bar duniyar nan a safiyar yau (Talata), ya bar ramin da zai yi wahalar cikawa.
Marigayin fitaccen ma’aikacin banki ne kuma shugaba wanda ya taba rike mukamin babban darektan tsofaffin bankunan zamanin da biyu.
Baffa ya taba zama shugaban kamfanin NSPMC kafin ya yi ritaya a karshe a shekarar 1999.
- Gwamna Umar Namadi
Farfesa Umaru Shehu ya rasu
Ana haka ne kuma sai ga labarin rasuwar shahararren malami kuma kwararren likita a Arewa, Farfesa Umaru Shehu ya na mai shekara 97.
Umaru Shehu ya na cikin wadanda su ka kafa kungiyar dattawan jihar Borno, mutuwarsa ta jawo makoki daga Arewa har kudancin kasar.
Barnar 'Yan Boko Haram
Lamarin ‘Yan Boko Haram ya na neman rikida kwanan nan, an ji labari 'yan ta'addan sun rama harin da sojoji su ka kai masu a kauyen Borno.
Da karfi da yaji mayakan na Boko Haram su ka dauke sarakunan gargajiya biyu a makon jiya, abin ya faru ne a wani kauye mai suna Burum.
Asali: Legit.ng