Yan Bindiga Sun Halaka Kansila a Jihar Katsina a Wani Sabon Hari
- Ƴan bindiga sun kai wani sabon hari a garin Funtua na jihar Katsina inda suka halaka mutum ɗaya
- Miyagun ƴan ta'addan sun halaka kansilan da ke wakiltar mazaɓar Nasarawa a garin na Funtua
- Mazauna unguwar sun kuma tabbatar da cewa ƴan bindiga sun sace wani mutum ɗaya bayan halaka kansilan
Jihar Katsina - Wasu ƴan bindiga kimanin mutum 20 sun kai farmaki garin Funtua, s daren ranar Litinin, inda suka kashe kansila mai wakiltar mazaɓar Nasarawa, Samaila Buhari Mairago.
Lamarin dai a cewar mazauna unguwar Nasarawa da ke Funtua, ya auku ne da misalin karfe 9:00 na dare, cewar rahoton Daily Trust.
A cewar mazauna unguwar, marigayin ya dawo ne daga ofishin ƴan sanda inda ya amso bindigarsa domin yin aikin sintiri a matsayin ɗaya daga cikin jami’an tsaron da gwamnatin jihar Katsina ta horas da su kwanan nan.
Yadda harin ya auku
Malam Musa Maibulo, makwabcin marigayi kansilan, ya ce ga dukkan alamu ƴan bindigar na shirin sace wani ne a unguwar, inda ya bayyana cewa marigayin ƙarar kwana ce ta auka masa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kalamansa:
"Babu wanda ya lura da wata barazana yayin da muke gudanar da harkokinmu na yau da kullum, abin da ba mu sani ba shi ne miyagun sun fake a cikin unguwarmu suna jiran lokaci ya yi su aikata ɓarna."
"Kansilan mu, Samaila Buhari wanda yana ɗaya daga cikin masu aikin samar da tsaro, ya je ofishin ƴan sanda na Makera domin karɓo bindigarsa saboda sintirin dare. Abin takaici, yana ƙoƙarin shiga gidansa ƴan bindigan suka lura da bindigar da ke tare da shi sai suka buɗe masa wuta."
Yan bindigan sun sace mutum ɗaya
Maibulo ya kara da cewa ƴan bindigan sun yi awon gaba da bindigar bayan sun kashe kansilan.
"Nan da nan bayan harbe-harben, ƴan bindigan sun ranta a na kare. Amma bayan sun tsere mun fahimci cewa sun sace wani makwabcinmu mai suna Malam Samaila Maikatako." A cewarsa.
Abbas Ismail, kawun marigayi kansilan ya ce marigayin ya bar mata ɗaya da ƴaƴa takwas.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Aliyu, ya tabbatar da aukuwar ƙmarin, inda ya ce sun fara gudanar da bincike, rahoton The Punch ya tabbatar.
Ana fama da rashin tsaro a Funtua
Abdulrahman Nasir wani mazaunin garin Funtua ya shaidawa Legit Hausa cewa matsalar rashin tsaro a garin Funtua kullum ƙara taɓarɓarewa take yi.
Ya bayyana cew a baya ƴan bindiga sai dai su tsaya wajen gari su yi ta'asarsu amma yanzu lamarin ya kai har cikin garin shigowa suke yi.
Ya koka kan yadda jajircewar jami'an tsaro ta yi ƙaranci wajen magance matsalar wacce ke neman zama ruwan dare.
VC Na UDUS Ƴa Musanta Harin Yan Bindiga
A wani labarin kuma, VC na jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto (UDUS), ya musanta cewa ƴan bindiga sun kai farmaki a harabar jami'ar.
Farfesa Lawal Bilbis ya bayyana cewa ƴan fashi ne suka yi sata a wasu shagunan makarantar ba ƴan bindiga ba kamar yadda aka yi ta yaɗa wa.
Asali: Legit.ng