Kotu Ta Ci Dan Takarar Labour Party Tarar N200 000 Kan Karar Da Ya Shigar Da Dan Majalisar PDP
- Kotun zaɓen ƴan majalisar dokokin jihar Abia ta yi fatali da ƙarar da ɗan taƙarar Labour Party ya shigar kan ɗan majalisar PDP na Obingwa ta Gabas
- Kotun ta tabbatar da nasarar Solomon Akpulonu a matsayin sahihin ɗan majalisa mai wakiltar Obingwa ta Gabas a majalisar dokokin jihar
- Kotun ta kuma ci tarar N200,000 kan Peter Azibuike na LP saboda rashin cancantar ƙarar da ya shigar
Jihar Abia - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisar dokokin jihar Abia, da ke zamanta a Umuahia, ta tabbatar da nasarar Honorabul Solomon Akpulonu, ɗan majalisar dokoki na jam'iyyar PDP mai wakiltar mazabar Obingwa ta Gabas a majalisar dokokin jihar Abia.
Kotun ta yi watsi da ƙarar da Peter Azubuike na jam'iyyar Labour Party (LP) ya shigar yana ƙalubalantar nasarar Akpulonu na jam'iyyar PDP a zaɓen na ranar 18 ga watan Maris, cewar rahoton jaridar The Nation.
A cikin ƙarar da ya shigar, Azubuike ya yi zargin cewa an kaɗa ƙuri’a fiye da ƙima a zaɓen inda ya buƙaci kotun da ta soke zaɓen tare da ba da umarnin sake zaɓe a rumfunan zaɓe 28.
Dan takarar na jam'iyyar Labour ya ce zaben da ya samar da Akpulonu a matsayin ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Obingwa ta Gabas bai dace da dokar zaɓe ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa kotun ta yi fatali da ƙarar?
Sai dai mai shari’a Abubakar Idris Kutigi wanda ya jagoranci alƙalan kotun, ya ce ƙarar da jam’iyyar Labour ta shigar ba ta cancanta ba, kuma mai shigar da ƙara ya kasa nuna inda aka yi aringizon ƙuri'a ko rashin amfani da dokar zaɓe.
Daga nan sai Kutigi ya ayyana Akpulonu na PDP a matsayin sahihin wanda ya lashe zaɓen sannan kuma ya ci tarar N200,000 ga dan takarar jam’iyyar Labour Party, wacce zai bayar ga ɗan takarar PDP
Da yake zantawa da manema labarai bayan yanke hukuncin, ɗan takarar na PDP ya yabawa kotun tare da bayyana hukuncin a matsayin sahihi wanda aka yi adalci.
Ya buƙaci Azibuike wanda ya kira a matsayin ɗan'uwa da ya zo su haɗa hannu su ciyar da mazaɓar gaba.
Kotu Ta Ci Abba Gida-Gida Tara
A wani labarin kuma, wata babbar kotun tarayya ta ci tarar gwamnan Kano, Abba Ƙabir Yusuf N30bn.
Kotun ta ci gwamnan wannan tarar ne a sakamakon ruguza shagunan wasu ƴan kasuwa da ya yi filin masallacin Idi na birnin Kano
Asali: Legit.ng