Fasto Fabian Nna Na Najeriya Ya Tayar Da Matattu? Gaskiya Ta Fito

Fasto Fabian Nna Na Najeriya Ya Tayar Da Matattu? Gaskiya Ta Fito

  • Ana zargin wani Fasto da ke zaune a birnin Port Harcourt, fasto Fabian Nna, ya tayar da wani mataccen mutum a cocinsa
  • Bidiyon da ake zargin na tashin matattun ne ya yadu a kafafen sada zumunta da suka hada da X (wanda a baya aka sani da Twitter) da Facebook
  • Sai dai, an gano cewa, tashin matattun, wani wasan kwaikwayo ne da ƙungiyar wasan kwaikwayo ta cocin suka yi

Port-Harcourt, Jihar Rivers - Cikakkun bayanai sun bayyana game da tashin wani mataccen mutum da wani fasto ya yi mai suna fasto Fabian Nna na cocin Fire of Liberation Interdenominational Ministries, a birnin Port-Harcourt na jihar Rivers.

Bidiyon tashin matattun ya yaɗu ne a kafafen sada zumunta da suka hada da X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) da Facebook, a ƙarshen makon nan.

Kara karanta wannan

Mummunan Hatsarin Mota Ya Ritsa Da Bayin Allah, Mutane Da Dama Sun Jikkata

Fasto Fabian Nna bai tayar da matacce ba
Ba gaskiya ba ne cewa fasto Fabian Nna ya tayar da matacce Hoto: Apostle Fabian Nna Ministries
Asali: Facebook

A cewar FIJ, a cikin faifan bidiyon, an nuna wani matashi sanye da fararen kaya a cikin wata ƴar karamar akwati wacce aka ajiye gaban mahalarta cocin.

An nuna wasu maza biyu da mace ɗaya a tsaye kamar wasu dogarai a kusa da akwatin yayin da faston ya yi magana da ƴan cocin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, wata budurwa a gefen dama na dandalin, wacce ta yi kamar ɗiyar mutumin da ake zaton ya mutu, ta yi magana cikin tausayi.

"Waye zai siya min shawarma da kaza da chips?" Budurwa ta tambaya yayin da wata ƴar cocin mace ta riƙe ta da ƙarfi.

Fasto Fabian Nna bai tayar da matattu ba

Tabbatar da sahihancin tashin matattu ta shafin facebook na faston, ya nuna cewa wasan kwaikwayo ne da ƙungiyar wasan kwaikwayo ta cocin ta shirya.

Kara karanta wannan

Za a Fasa Shiga Yajin-Aiki a Najeriya, Gwamnati Ta Shawo Kan Kungiyoyin Ma’aikata

An shirya wasan kwaikwayon ne yayin hidimar cocin na kwanaki 3 mai taken Ebenezer 2023 daga ranar 30 ga watan Satumba zuwa ranar 2 ga watan Oktoba.

Fasto Ya Kasa Tafiya Baya Yin Azumi

A wani labarin kuma, wani fasto ya ta kansa bayan ya kwashe kwanaki yana yin azumi ba ƙaƙƙautawa a jihar Delta.

Fasto Victor Great wanda shi ne babban faston cocin Zion Ark of Covenant Int’l Bible Church Inc. a jihar Delta, ya tsinci kansa cikin wannan halin ne bayan ya kwashe kwanaki 21 yana azumi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng