Balarabe Abbas Lawal: Tarihin Wanda Zai Canji El-Rufai a Kujerar Ministan Kaduna
- Balarabe Abbas-Lawal ya kama hanyar zama sabon Minista a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu
- Sakataren na gwamnatin jihar Kaduna zai maye gurbin mutuminsa wanda majalisa ta ki tantacewa
- Malam Lawal ya yi sama da shekaru takwas ya na kan kujerar sakataren gwamnati a jihar Kaduna
Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya zabi Balarabe Abbas-Lawal domin ya zama wanda zai wakilci jihar Kaduna a majalisar zartarwa watau FEC.
Legit.ng Hausa ta tattaro gajeren bayani game da tarihin sakataren gwamnatin Kadunan.
Wanene Balarabe Abbas Lawal?
1. An haifi Abbas Lawal ne a Fubrairun 1958, yanzu haka ya na da shekaru 65 a duniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2. Tsakanin 1964 da 1970 ya halarci makarantar firamare ta gwamnati a Kofar Kuyambana a Zariya.
3. A shekarar 1971 ya shiga makarantar Baewa College, hakan ya ba shi damar haduwa da Nasir El-Rufai.
4. Ministan na gobe ya yi sharar fage a makarantar da ake kira Katsina College of Arts, Science and Technology.
5. Zuwa 1981, sai ga Balarabe Abbas Lawal ya samu shaidar digiri a ilmin kimiyyar siyasa daga jami’ar ABU Zariya.
6. Baya ga digirin farko, ya sake komawa jami’ar domin yin digiri na biyu watau M.Sc duk a ilmin siyasa.
7. Lawal ya yi kwas iri-iri kama GMC, ASCON, MTC, CFED, IP3, IVLP a Legas, Amurka, Ingila, Kanada da sauransu.
8. Karatun da ya samu a Thames Valley College da jami’o’i irinsu Harvard sun taimaka masa wajen zama malami.
9. A baya ya yi aiki da kamfanonin ASCON da NEPA da gwamnatin tarayya ta rusa su a shekarun baya.
10. A lokuta dabam-dabam, Malam Balarabe Abbas Lawal ya yi aiki da ministocin ilmi da na tsaro a Najeriya.
11. Yayin da Nasir El-Rufai yake ministan harkokin birnin Abuja, shi ne shugaban ma’aikatan fadarsa.
Balarabe Abbas Lawal a gwamnatin Kaduna
12. Lawal ya jagoranci aikin mika mulki a gwamnatin jihar Kaduna bayan zabukan 2015 da na 2023.
13. A sakamakon nasarar El-Rufai a zaben 2015, sai ya dauko tsohon hadiminsa domin zama sakataren gwamnati.
14. Bayan tazarce da APC ta yi a 2019, Lawan ya cigaba da zama a kan kujerar sakataren gwamnatin Kaduna.
15. Ko da Uba Sani ya karbi mulki, ya bar Abbas-Lawal a kujerarsa domin ganin ya sa kan aiki a jihar Kaduna.
Nasir El-Rufai bai dace ba
Idan Balarabe Abbas Lawal ya samu amincewar majalisar dattawa, zai rike kujerar da mai gidansa, Malam Nasir El-Rufai bai iya komawa kai ba.
Ku na da labarin abubuwan da su ka jawo 'yan majalisa su ka ki amincewa tsohon gwamnan Kaduna ya zama minista a gwamnatin Bola Tinubu.
Asali: Legit.ng