'Yan Bindiga Sun Shiga Jami'ar Usman Ɗanfodio Da Ke Jihar Sakkwato
- Wasu ɓarayi sun shiga jami'ar Usman Ɗanfodiyo da ke jihar Sakkwato sun kwashi kayan abinci da wasu kayayyaki
- Shugaban jami'ar, Farfesa Lawal Bilbis, ya musanta rahoton da ake yaɗa cewa 'yan bindiga ne suka kai farmaki
- Wani ɗalibin UDUS ya shaida wa Legit Hausa cewa ɓarayi ne kawai suka shigo suka saci kayayyaki a kasuwar makaranta
Jihar Sokoto - Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton ɓarayi ne sun kai farmaki jami'ar Usman Ɗanfodiyo da ke jihar Sakkwato ranar Litinin 2 ga watan Oktoba, 2023 da daddare.
Rahoton TRT Hausa ya tattaro cewa maharan sun kutsa kai cikin ƙaramar kasuwar makaranatar wacce ake kira, 'Mini Market' inda suka kwashe kayayyaki da dama.
Shugaban jami'ar UDUS, Farfesa Farfesa Lawal Suleiman Bilbis, ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin jaridar.
Ya ce maharan sun kwashi kayan abinci da sauran abubuwa masu yawa a ƙasuwar ta Mini Market yayin harin na daren jiya Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai bayanai sun nuna cewa jami'ar tsaron jami'ar Ɗanfodiyon sun samu nasarar daƙile harin, inda suka fatattaki maharan baki ɗaya.
Jaridar TRT Hausa ta wallafa a shafinta na Facebook cewa:
"Yan bindiga sun shiga Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto (UDUS) ranar Litinin da daddare inda suka je kasuwar mini market suka kwashi kayan abinci da sauran abubuwa," in ji shugaban Jami'ar Farfesa Lawal Suleiman Bilbis.
Gaskiyar abinda ya faru a UDUS
Sabanin abinda ake yaɗa wa, Farfesa Lawal Bilbis, a wani taron manema labarai a ofishinsa ranar Talata, ya ce harin na fashi ne, ba wai harin ‘yan bindiga ba, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Farfesa Bilbis, ya yi kira ga mutanen Jami’ar da kuma iyaye da su kwantar da hankalinsu, yana mai cewa “babu wani abin damuwa game da tsaron rayukan daliban jami’ar.
Wani ɗalibin jami'ar, Muhammad Jabir, ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin Legit Hausa ta wayar Salula.
Ya ce ɓarayi ne suka shigo suka yi sata a kasuwa amma ba 'yan bindiga ba kamar yadda ake yaɗa wa a wasu kafafen sada zumunta.
"Eh na ga wasu na cewa 'yan bindiga, a zahirin gaskiya ba su bane, ɓarayi ne da aka sani suka shigo suka ɗibi kayan abinci a kasuwa, ba su shiga ɗakunan ɗalibai ba, Allah ya ƙara tsare mu."
Borno: Jirgin Sojin Sama Ya Ragargaji Yan Ta'adda da Yawa a Yankin Tafkin Chadi
A wani rahoton kuma Jirgin NAF ya halaka gomman mayaƙan ƙungiyoyin 'yan ta'adda.yayin da ya kai samamen ruwan wuta ta sama a Tafkin Chadi.
Kakakin NAF na ƙasa ya bayyana cewa luguden wutan ya yi fata-fata da maɓoyar yan ta'addan tare da lalata kayan aikinsu.
Asali: Legit.ng