Shehu Sani Ya Yabawa BUA Kan Rage Farashin Siminti, Ya Roki Masu Abinci Su Yi Koyi Da Shi

Shehu Sani Ya Yabawa BUA Kan Rage Farashin Siminti, Ya Roki Masu Abinci Su Yi Koyi Da Shi

  • Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya yabawa mai kamfanin BUA kan rage farashin siminti da ya yi a dai-dai lokacin da ake cikin wani hali
  • Sani ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a jiya Litinin 2 ga watan Oktoba inda ya ce wannan abin yabawa ne a kasar
  • Sanatan ya kuma ce ba a taba ganin irin haka ba a Najeriya inda ya roki masu siyar da kayan abinci su yi koyi da BUA

Jihar Kaduna - Sanata Shehu Sani ya yabawa mai kamfanin BUA kan rage farashin siminti zuwa Naira 3,500 a Najeriya.

Kamfanin BUA wanda shi ne na biyu a kasar wurin samar da siminti ya ce za a fara siyar da simintin kan sabon farashin daga ranar 2 ga watan Oktoba, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Muhammadu Buhari: Babban Sakona Ga Mutanen Najeriya a Ranar Murnar 'Yancin Kai

Shehu Sani ya yabawa kamfanin BUA kan rage farashin siminti
Shehu Sani Ya Yi Martani Bayan BUA Ya Rage Farashin Siminti. Hoto: Shehu Sani.
Asali: Facebook

Meye Shehu Sani ya ce kan rage farashi na BUA?

Kamfanin ya dauki wannan matakin ne yayin da Dala ke kara tashi da kuma halin da 'yan Najeriya ke ciki a wannan yanayi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sani ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter inda ya ce wannan abin yabawa ne kuma wanda ba a taba ganin irin shi ba.

Har ila yau, ya roki masu siyar da kayan abinci da su kwaikwayi hali irin na BUA don rage wa mutane radadin rashin farashin kaya a kasar.

Ya rubuta kamar haka:

"Duk da tashin farashin Dala, BUA ya rage kudin siminti, wannan abin a yaba ne kuma wanda ba a taba ganin irin shi ba.
"Mu na fatan wannan ba talle ba ce, ina kira ga masu siyar da abinci su kwaikwayi hali irin na BUA."

Kara karanta wannan

Kama Da Wane: Mutum Da Ya Sauya Siffarsa Zuwa Ta Kare Ya Shiga Tasku, Ya Ce Karnuka Ba Sa Wasa Da Shi

Wane sako kamfanin BUA ya fitar kan rage farashin siminti?

Kamfanin ya bayyana cewa ya rage farashin ne don inganta harkokin gine-gine a kasar da kuma samun sauki.

Ya ce da zarar an kammala sabon kamfaninsu wanda zai na samar da siminti tan miliyan 17, za su sake rage farashin siminti a farkon shekarar 2024.

Kamfanin BUA ya rage farashin siminti

A wani labarin, Kamfanin siminti na BUA ta rage farashin siminti zuwa Naira 3,500.

Wannan mataki na zuwa ne yayin da 'yan Najeriya ke cikin matsin tattalin arziki da wahalhalu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.