Kungiyoyin Kwadago Sun Soke Tafiya Yajin Aiki Bayan Ganawa Da Gwamnatin Tarayya
- Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun jingine batun tafiya yajin aikin sai baba ta gani da suka shirya
- Hakan ya biyo bayan tattaunawar da aka shafe tsawon lokaci ana yi tsakanin tawagar gwamnatin tarayya da shugabannin kwadagon
- Bayan cimma wasu yarjejeniya da suka hada da karawa ma'aikata albashin N35,000 kungiyar kwadagon ta janye zuwa yajin aiki nan da kwanaki 30
Daga karshe shugabannin kungiyoyin kwadago na kasa NLC da TUC sun janye tafiya yajin aikin sai baba ta gani da suka shirya zuwa, wanda ya kamata ya fara daga ranar Talata, 3 ga watan Oktoba.
kungiyoyin kwadagon sun sanar da soke tafiya yajin aikin ne a cikin wata sanarwa da suka saki bayan ganawarsu da wakilan gwamnatin tarayya a fadar shugaban kasa a ranar Litinin, 2 ga watan Oktoba.
Dan Kasuwa A Kano, Dantata Ya Kirkiro Bankin Yanar Gizo Da Zai Yi Gogayya Da Opay, Kuda, Ya Dauki Alkawari
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Cikakkun bayanai kan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnatin tarayya da shugabannin kwadago
Ga jerin yarjejeniyar da aka cimmawa tsakanin gwamnatin tarayya da shugabannin kwadago bayan tattaunawarsu don hana tafiya yajin aiki.
1. Gwamnatin tarayya ta amince da biyan 35,000 ga dukkan ma'aikatan gwamnati daga watan Satumba zuwa lokacin da ake sa ran sanya hannu a sabon mafi karancin albashi na kasa.
2. Za a kaddamar da kwamitin tsara mafi karancin albashi cikin wata daya daga ranar da a ka kulla wannan yarjejeniya.
3. Gwamnatin tarayya ta janye harajin VAT a man Dizal na tsawon wata shida farawa daga watan Oktoban 2023.
4. Gwamnatin tarayya ta amince da naira biliyan 100 don gaggauta samar da motoci masu amfani da gas don saukaka matsalolin sufuri.
5. Gwamnatin Tarayya na shirin aiwatar da matakai daban-daban na karfafa haraji ga kamfanoni masu zaman kansu da sauran jama'a.
6. Dangane da rigingimun shugabanci da ya dabaibaye kungiyar NURTW da kuma zargin haramtawa RTEAN, Gwamnatin Tarayya ta himmatu wajen tafiyar da al’amuran Ma’aikata daidai da Yarjejeniyar ILO da Dokar Kwadago ta Najeriya. Ana sa ran za a warware rikicin da ke gudana nan da 13 ga Oktoba.
7. An mika batun albashin da ma'aikatan jami'o'in tarayya ke bi ga ma'aikatar kwadago da daukar ma'aikata don ci gaba da tattaunawa.
8. Gwamnatin tarayya ta yanke shawarar rabawa gidaje miliyan 15 tallafin N25,000 na tsawon wata uku, fara daga watan Oktoban 2023.
9. Gwamnatin tarayya za ta kara kaimi wajen rabon tallafin takin zamani ga manoma a fadin kasar.
10. Ya kamata gwamnatin tarayya ta bukaci gwamnonin jiha ta majalisar tattalin arziki na kasa da kungiyar gwamnoni da su aiwatar da karin albashin ga ma'aikatansu. Haka kuma ya kamata a yi hakan ga ma'aikatan karamar hukuma da kamfanoni masu zaman kansu.
11. Gwamnatin tarayya ta himmatu wajen samar da kudade ga masu kananan sana'o'i kamar yadda shugaban kasar ya sanar a jawabinsa na ranar 1 ga watan Agusta.
12. Za a gudanar da ziyarar hadin gwiwa a matatun mai domin tabbatar da matsayin gyaransu.
13. Dukkan bangarorin sun kuduri aniyar ci gaba da bin ka'idojin sulhu a duk ayyukanmu na gaba.
14. Kungiyoyin NLC da TUC sun amince da dakatar da yajin aikin sai baba ta gani da suke shirin farawa a ranar Talata, 3 ga watan Oktoban 2023 na tsawon kwanaki 30.
15. Za a gabatar da takardar yarjejeniya da bangarorin suka sa hannu ga kotun da ta dace cikin mako guda a matsayin hukuncin da gwamnatin tarayya ta amince da shi.
Shugaba Tinubu ya karawa ma’aikata alawus a yunkurin hana ‘yan kwadago yajin aiki
A baya mun ji cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya na bakin kokarinsa na ganin an daina maganar shiga yajin-aikin da sai baba-ta-gani a kasar nan.
Sanarwa ta fito daga fadar shugaban kasar cewa an amince ayi wa ma’aikatan gwamnatin tarayya karin N10, 000 kan alawus din da za a raba.
Asali: Legit.ng