Sakon Da Na Ke Da Shi Ga ‘Yan Najeriya a Ranar ‘Yancin Kai, Muhammadu Buhari
- Muhammadu Buhari ya zanta da manema labarai a yayin da Najeriya ta cika shekara 63 da ‘yanci
- Tsohon shugaban kasar ya yi maganar cigaba da aka samu ta fuskar siyasa a shekarun bayan nan
- Janar Buhari bai da wata shawara ga mutane da ta wuce su zama masu yawan hakuri da junansu
Katsina - Muhammadu Buhari ya yi wata hira da manema labarai domin jin ta bakinsa yayin da ake bikin murnar samun ‘yancin-kai.
A rana irinta jiya watau 1 ga watan Oktoba a 1960, Najeriya ta samu ‘yanci daga hannun Turawan mulkin mallaka na kasar Birtaniya.
Da aka zanta da shi kamar yadda DCI Hausa ta tsakuro hirar, Muhammadu Buhari ya yi kira ga al’ummar da ya mulka har na shekaru takwas.
Muhammadu Buhari ya ce talaka ya waye
Mai girma Muhammadu Buhari ya yi magana a kan yadda aka samu cigaba ta fuskar siyasa, ya na mai ganin talaka ya kara wayewa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Janar Buhari mai ritaya ya ce yadda tsofaffin gwamnoni su ka gaza zama Sanatoci a zaben 2023 ya nuna idon masu zabe ya bude a yau.
A ra’ayin tsohon shugaban kasar, matasa su na da dalilin yin fushi da Najeriya, amma ya yi kira da a cigaba da yin hakuri da juna.
Abin da ya faru da tsofaffin Gwamnoni
"Ku dubi kudin da ake samu a da, da lokacin da mu ka zo, sai da mu ka taimakawa jihohi su ka biya albashi da kuma fansho.
Amma bayan gwamnonin nan goma sun yi shekaru takwas a jihohinsu, sai su ka so su tafi majalisar dattawa, amma mazabunsu su ka ki zaben su.
Wannan shi zai nuna maka ‘Yan Najeriya sun fahimci siyasa, kuma idan za ayi ta sosai, za su yi abin da su ka ga dama."
- Muhammadu Buhari
A rika yin hakuri da juna - Buhari
Da aka tambaye shi game da sakon da yake da shi ga al’umma a ranar da ake murna da samun ‘yancin kai, sai ya ce a rika hakuri.
"Ni babban sako na shi ne mu yi hakuri da juna. Allah ya azurta kasar nan, ban san ko Najeriya sun yi tunanin mu na ina yanzu idan da sayen mai mu ke yi."
- Muhammadu Buhari
Abdullahi Adamu, Tinubu da zaben 2023
Kun ji tsohon shugaban APC, Abdullahi Adamu ya ce bai yi nadamar nasarar Bola Tinubu a zaɓen 2023 ba duk da bai tare da shi da farko.
Sanata Adamu ya bayyana cewa ya ji daɗi da Tinubu ya gaji Muhammadu Buhari,. Daga baya sai aka ji ya yi murabus daga kan kujerarsa.
Asali: Legit.ng