An Samu Asarar Rai a Wani Hatsarin Mota a Hanyar Legas-Ibadan

An Samu Asarar Rai a Wani Hatsarin Mota a Hanyar Legas-Ibadan

  • Wani mummunan hatsarin mota ya ritsa da mutane masu yawa a kan titin hanyar Legas zuwa Ibadan
  • Mutum ɗaya ya riga mu gidan gaskiya yayin da wasu fasinjoji bakwai suka samu raunika a harin da ya auku a tashar motar Magboro
  • Hukumomi sun tabbatar da aukuwar hatsarin inda suka ɗora alhakin aukuwarsa kan ajiye motoci a kan hanya da gudu wanda ya wuce ƙima

Jihar Ogun - Wani mutum da har yanzu ba a tantance ko wanene ba ya mutu a ranar Lahadi, 1 ga watan Oktoba, a wani hatsarin da ya ritsa da mutuem 16 a tashar mota ta Magboro da ke kan hanyar Legas zuwa Ibadan.

Rahotanni sun ce wasu fasinjoji bakwai sun jikkata a hatsarin da ya auku da misalin karfe 7:50 na safe.

Kara karanta wannan

Za a Fasa Shiga Yajin-Aiki a Najeriya, Gwamnati Ta Shawo Kan Kungiyoyin Ma’aikata

Mutum daya ya rasu a wani hatsarin mota a jihar Ogun
Motocin da hatsarin ya ritsa da su Hoto: Punchng.com
Asali: UGC

Jaridar The Punch ta tattaro cewa motoci biyu, ɗaya ƙirar Mercedes Benz ML350 mai lamba AKD424HH da wata motar bas ta kasuwanci ƙirar Volkswagen mai lamba KSF934YA, su ne suka yi hatsarin.

Yadda hatsarin ya auku

A cewar wata ganau ba jiyau ba mai suna Opeyemi Lateef, hatsarin ya auku ne a lokacin da motar Mercedes Benz ta yi karo da wata motar bas ta kasuwanci da ke ajiye a tashar motar a lokacin da take ƙoƙarin kaucewa wani da zai tsallaka hanya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamanta:

"Abin da ya faru shi ne, direban motar Benz ɗin ya yi ƙoƙarin kaucewa buge wani da ya zo tsallaka titi, wanda hakan ya sanya ta ƙwace masa, inda ya yi karo da motar bas ɗin a lokacin da direbanta ke jiran fasinjoji a tashar motar."

Wani shaidan gani da ido da ya nemi a sakaya sunansa ya alakanta musabbabin hatsarin da ajiye motoci ba bisa ƙa'ida ba a tashar motar da gudu wanda ya wuce ƙa'ida.

Kara karanta wannan

Yadda Mahaifiya Ta Yi Ta Maza Ta Cafke Dan Ta'addan Da Ya Yi Garkuwa Tare Da Halaka Yarta

Menene abin da hukumomi suka ce?

Da aka tuntubi jami'ar hulda da jama’a ta hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa reshen jihar Ogun, Florence Okpe, ta tabbatar da aukuwar hatsarin, inda ta danganta aukuwar hatsarin da gudu wanda ya wuce ƙima.

A kalamanta:

"Eh tabbas hatsarin ya auku da misalin ƙarfe 7:50 na safe a kan titin Legas zuwa Ibadan a tashar Magboro."
"Mutum16 ne da suka haɗa da maza takwas da mata takwas hatsarin ya ritsa da su. Mutum bakwai sun jikkata yayin da mutum ɗaya ya mutu."

Ta yi Allah wadai da yadda ake ajiye motocin ƴan kasuwa a kan manyan tituna, inda ta bayyana lamarin a matsayin babban musabbabin hadarurruka a tashar Magboro.

Hatsarin Mota Ya Ritsa Da Shugaban Majalisa

A wani labarin kuma, shugaban majalisar dokokin jihar Osun ya tsallake rijiya da baya a wani hatsarin mota da ya ritsa da shi.

Adewale Egbdedun da ayarin motocinsa sun gamu da hatsarin ne lokacin da suke ƙoƙarin barin birnin Osogbo, babban birnin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng