Wike Ya Caccaki Ma’aikata Da Ke Zanga-Zanga Kan Tsige Shugabannin Hukumomi
- Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi martani kan bidiyon masu zanga-zanga kan tsige shugabannin kamfanoni da hukumomi a FCT
- Wike ya ce tausayi da son zuciya ba za su taba hana shi yin abun da yake shine daidai ba don ra'ayin yan Najeriya
- Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya ce ko shi da yake minista ana iya tsige shi don haka kada masu rike da mukaman siyasa su shagala da yawa
Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce babu wani tunani ko tausayi da zai hana shi yin abun da yake shine daidai, rahoton The Cable.
Wike ya bayyana hakan ne a Abuja, yayin da yake martani ga wani bidiyo da ke yawo na ma'aikatan kamfanin sufuri (AUMTCO) da ke kokawa kan tsige manajan daraktan kamfanin.
Shugaban kamfanin, Mista Najeeb Abdulsalam, yana cikin shugabannin hukumomi da kamfanonin hukumar FCT 21 da ministan ya tsige a ranar Laraba.
Zan ci gaba da yin abun da ya dace a Abuja, Wike
Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya bayyana cewa zai yi abun da ya dace saboda ra'ayin mazauna babban birnin tarayya da yan Najeriya baki daya, rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wike ya ce:
"Wannan ne dalilin da yasa idan na kalli mutane a bidiyo, suna kukan cewa an tsige wani sannan cewa yana kokari, amma tambayar a nan ita ce, idan kana kokari, ina motocin?
"Babu son zuciya, babu tausayi da za a yi la'akari da shi idan muna yin abun da yake shine daidai. Za mu yi abun da ya dace don ra'ayin mutane. Idan kun so, ku dauko mutum 20, ku sa bidiyo sannan ku yi kuka yadda kuke so, ba zai dame mu ba. Abun da ke damunmu shine zahirin gaskiya da ke kasa."
Ko ni za a iya raba ni da mukamin minista, Wike ga masu zanga-zanga
Ya shawarci wadanda aka bai wa mukaman siyasa da su shirya barin ofis a koda yaushe saboda wani na iya zuwa kuma zai so kawo sauyi gaba daya.
Ya kara da cewa:
"Kai ba ma'aikacin gwamnati bane inda za ce bai kamata wani ya yi mun ritaya ba saboda ban kai shekarun ritaya ba.
"Hatta ni da nake matsayin minista. Ana iya raba ni da mukamina yanzu. Ba ku bukatar kuka; wasu mutanen ma za su zo kuma abun da muke addu'a shine, mu yi iya bakin kokarinmu."
Tinubu ya karawa ma'aikata gaba daya albashin N25,000
A wani labarin, mun ji cewa sShugaban kasa Bola Tinubu ya amince da karin albashin wucin gadi na N25,000 ga ma'aikata a dukkan matakai.
Kamar yadda NTA News ta rahoto, Shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, ne ya sanar da hakan bayan ganawar da gwamnatin tarayya ta yi da shugabannin kungiyar kwadago.
Asali: Legit.ng