Kungiyar Kwadago Na Sa Labule Da Gwamnatin Tinubu a Fadar Villa
- Gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago sun shiga ganawar sirri a fadar shugaban kasa da ke Abuja
- Taron na ranar Lahadi, 1 ga watan Oktoba na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyoyin kwadago na kasar ke shirin shiga yajin aiki
- Kungiyar NLC dai ta yanke shawarar fara yajin aikin sai baba ta gani daga ranar Talata, 3 ga watan Oktoba
Abuja - A yanzu haka shugabannin kungiyar kwadago na cikin ganawa da tawagar gwamnatin tarayya a fadar shugaban kasa da ke Abuja, gabannin fara yajin aikin gama gari na har sai baba ta gani.
Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC), Joe Ajaero, ne ke jagorantar tawagar yan kwadago.
Legit Hausa ta tattaro cewa sakataren kungiyar kasuwanci na kasa (TUC) Nuhu Toro da takwaransa na NLC, Emma Ugbaja, suma sun halarci taron.
Manyan jami'an gwamnati sun halarci ganawar FG da kungiyar kwadago
Shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ne ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran tawagar gwamnati sun hada da Shugaban ma'aikatan tarayya, Dr. Folasade Yemi-Esan, babban mai ba kasa shawara kan harkokin tsarom Mallam Nuhu Ribadu, ministan kwadago da daukar ma'aikata, Simon Lalong, da karamar ministar kwadago, Nkeiruka Onyejecha.
Sai kuma ministan kudi, Wale Edun, Ministan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki, Atiku Bagudu da ministan harkokin jin kai da kawar da talauci, Beta Edu duk sun hallara.
Jaridar Punch ta rahoto cewa wasu daraktoci daga ma'aikatar kwadago da daukar ma'aikata ma sun halarci zaman.
Kungiyar kwadago ta ce babu ja da baya a yajin aikin da take shirin zuwa
A baya mun ji cewa kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta bukaci daukacin al'ummar Najeriya da su shiga cikin "gangamin neman yanci", inda ta dage cewa za ta shiga yajin aikin sai baba ta gani daga ranar Talata.
Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Ya Sake Yin Wata Hubbasa 1 Domin Hana NLC Shiga Yajin Aiki Ranar Talata
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero, ya fitar a safiyar ranar Lahadi, 1 Oktoba, na bikin cikar kasar shekaru 63 da samun ‘yancin kai.
Ya sanar da yan Najeriya cewa za su cimma nasara idan suka tsaya tsayin daka a matsayin kungiya da ba za a iya raba kanta ba, Channels TV ta rahoto.
Asali: Legit.ng