Kungiyar Kwadago Ta Ce Babu Ja Da Baya a Yajin Aikin Da Take Shirin Zuwa

Kungiyar Kwadago Ta Ce Babu Ja Da Baya a Yajin Aikin Da Take Shirin Zuwa

  • Kungiyar NLC ta dage a kan kudirinta na tafiya yajin aikin sai baba ta gani a fadin kasar
  • Shugaban kungiyar kwadago na kasa, ya yi kira ga daukacin yan Najeriya da su shiga tattakin neman yanci da suke shirin farawa a ranar Talata, 3 ga watan Oktoba
  • Joe Ajaero ya ba da tabbacin samun nasara a tafiyar da za su yi idan har al'ummar kasar suka hada kansu waje guda

Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta bukaci daukacin al'ummar Najeriya da su shiga cikin "gangamin neman yanci", inda ta dage cewa za ta shiga yajin aikin sai baba ta gani daga ranar Talata.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero, ya fitar a safiyar ranar Lahadi, 1 Oktoba, na bikin cikar kasar shekaru 63 da samun ‘yancin kai.

Kara karanta wannan

N1000 Kowace KG: Yan Najeriya Sun Koka Kan Karin Farashin Gas Yayin da Kasar Ke Bikin Cika Shekaru 63

Ya sanar da yan Najeriya cewa za su cimma nasara idan suka tsaya tsayin daka a matsayin kungiya da ba za a iya raba kanta ba, Channels TV ta rahoto

Kungiyar kwadago ta ce babu gudu babu ja da baya a yajin aikin da za ta shiga
Kungiyar Kwadago Ta Ce Babu Ja Da Baya a Yajin Aikin Da Take Shirin Zuwa Hoto: NLC
Asali: Facebook

Kungiyar kwadago ta yi kira na musamman ga yan Najeriya yayin da take shirin fara yajin aiki

Ajaero ya bukaci dukkan masu masu fada aji a kasar, musamman masu rike da sarautun gargajiya da su roki gwamnati ta sauke nauyin da ke kan jama’a, rahoton The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ajaero ya ce:

"A tare, za mu iya dawo da darajar da ya kubce mana tsawon lokaci. Lokaci ya yi da Najeriya za ta tashi ta sake haskawa a matsayin fitilar fata da wadata ga daukacin al'ummarta.
"Ku tuna, idan muka tsaya a matsayin tsintsiya madaurinki daya muka hana a raba mu, za mu yi nasara! Muna kira ga daukacin yan Najeriya da su kasance tare da mu a ranar 3 ga watan Oktoba a fadin Najeriya domin fara tattakinmu na neman yanci ta hanyar yajin aikin gama gari har sai baba ta gani."

Kara karanta wannan

Dama-dama: Tinubu ya karawa ma'aikata albashi, amma akwai abin kura a gaba

Shugaban kungiyar kwadagon ya bukaci yan kasar da su yi bikin ranar ‘yancin kai tare da sabunta manufarsu.

Ya kara da cewar:

"Mu amince da abubuwan da suka gabace mu, mu tunkari kalubalen da ke gabanmu a yanzu. sannan mu hada hannu wajen samar da kyayyawar makoma ga Najeriya."

Yajin aiki: Gwamnatin Tinubu ta sake gayyatar kungiyoyin kwadago

A gefe guda, mun ji cewa gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu ta sake yunkurawa don dakatar da yajin aikin da kungiyoyin kwadago ke shirin shiga a ranar Tala.

Za a gudanar da taron ne ranar Lahadi, 1 ga watan Oktoba, da misalin ƙarfe 2:00 na rana fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng