Gyara Na da Zafi, Ya Kamata Ku Kure, Shugaba Tinubu Ga ’Yan Najeriya Ranar ’Yancin Kai

Gyara Na da Zafi, Ya Kamata Ku Kure, Shugaba Tinubu Ga ’Yan Najeriya Ranar ’Yancin Kai

  • Shugaba Tinubu ya bayyana cewa, ya fahimci irin radadin da ‘yan kasa ke ciki sakamakon cire tallafin man fetur a watan Mayu
  • Ya ce dole ne ‘yan Najeriya su jure wahalhalun da ake ciki sakamakon cire tallafin, ya ce yana sane da halin da kowa ke ciki a kasar
  • A jawabinsa, Tinubu ya bayyana karin albashi ga wasu ma’aikata a kasar nan na tsawon watanni shida masu zuwa nan gaba

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya ce akwai bukatar ‘yan Najeriya su jure wa kalubalen wahalar tattalin arziki da ake fama da shi a kasar nan domin samun ingantacciyar makoma.

A jawabin da ya yi na bikin cikar Najeriya shekaru 63 da samun ‘yancin kai a ranar Lahadi, Tinubu ya ce gyare-gyaren da ya sa a gaba za su ba da wahala amma gwamnatinsa na yin duk mai yiwuwa don kyautata rayuwar ‘yan kasa.

Kara karanta wannan

An samu sauki: Tinubu zai ware talakawa miliyan 15 ya raba musu kudi, ya fadi yaushe

Tinubu ya ce dole za a sha wahala kadin a gyara Najeriya
Gyara babu dadi, cewar Tinubu ga 'yan Najeriya | Hoto: Asiwaju Bola Ahmad Tinubu
Asali: Facebook

Shugaban ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatinsa ta bullo da shi zai dora al'ummar kasar kan turbar wadata da ci gaba a nan gaba.

Abin da Tinubu ke fadi

Wakilin Legit Hausa ya ji shugaban kasar na cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Na gamsu da wahalhalun da suka dumfaro. Ina da zuciya mai ji da idanu masu gani.
"Ina sona bayyana muku dalilin da ya sa dole mu jure wannan mawuyacin hali. Wadanda suka nemi dawwamar da tallafin man fetur da karya manufofin musayar kudaden waje mutane ne da za su gina manyan gidaje ga danginsu a doron kasar nan.
“Ni daban ne. Ni ba mutum ne da zan gina kasarmu a kan tubalin tabo ba. Domin mu jimre, dole ne mu gina gidanmu a kan kasa mai aminci kuma mai dadi.”

Shugaban ya tunatar da ‘yan kasa cewa, gyara akwai radadi, amma dole a jure matukar ana son ganin ci gaba a nan gaba.

Kara karanta wannan

Dama-dama: Tinubu ya karawa ma'aikata albashi, amma akwai abin kura a gaba

Za a karawa ma’aikata albashi

A wani labarin, jigo a jam’iyyar APC a jihar Zamfara, Dr Sani Shinkafi, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta yi watsi da batun gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal a kalaman da ya yi kan ganawar sirrin da aka yi tsakanin gwamnatin tarayya da ‘yan bindiga.

Ya kuma caccaki gwamnan da cewa, a matsayinsa na wanda ya dace ya wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jiharsa, shi ke kokarin kawo rudu ga lamarin tsaro, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.