Ku Dakatar da Shirin Shiga Yajin Aiki, Shugaban Majalisar Dattawa Ya Roki Kungiyoyin Kwadago

Ku Dakatar da Shirin Shiga Yajin Aiki, Shugaban Majalisar Dattawa Ya Roki Kungiyoyin Kwadago

  • Jigon siyasa a Najeriya ya bayyana kadan daga abin da ya gani na ci gaba a Najeriya
  • Ya bayyana bukatar masu ruwa da tsaki na kungiyar NLC da TUC da su janye batun yajin aiki
  • Hakazalika, ya yi kira ga 'yan Najeriya da su ba gwamnatin Tinubu hadin kai don a samu ci gaba

Yayin da Najeriya ke shirin bikin cika shekaru 63 da samun ‘yancin kai, shugaba a majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele, ya roki kungiyar kwadago ta Najeriya da ta dakatar da shirin shiga yajin aikin sai baba-ta-gani.

Bamidele ya yi nuni da cewa, gwamnatin tarayya da dukkan hukumomin da abin ya shafa suna aiki domin samar da hanyoyin da suka dace wajen magance bukatun kungiyoyin kwadago.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Bamidele ya taya 'yan Najeriya murnar cika shekaru 63 da samun 'yancin kai, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Mafita: Jigon APC ya ba da shawarwari 5 ga Tinubu don magance aukuwar yajin aiki

Ku yi hakuri ku janye yaji, sanata ga NLC
Sanata ya roki a janye yajin aiki | Hoto: Opeyemi Bamidele
Asali: Twitter

Najeriya na samun ci gaba tun 1960

Bamidele ya lura cewa Najeriya, daga ranar 1 ga Oktoba, 1960 zuwa yau, duk da kalubalen da take fuskanta na ci gaba da samun ci gaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika, ya ce 'yan kasar na ci gaba da kasancewa a inuwa daya duk da bambancin ra'ayi, addini da al'ada.

A cewarsa, tunda aka kafa sabuwar gwamnati ta Tinubu, 'yan kasar za su samu sauki nan kusa.

A ba gwamnatin Tinubu hadin kai

Hakazalika, ya ce duk dan Najeriya da ke ciki da wajen kasar zai ci gaba da alfahari da ita saboda sauyin da za a samar.

Daga nan ya roki 'yan kasar da su kasance masu hadin kai tare da ba gwamnatin Tinubu hadin kai don kawo ci gaba.

Karshe, ya yi kira ga kungiyoyin kwadago na TUC da NLC da su dakata da batun tafiya yajin aikin da suka tsara a mako mai zuwa.

Kara karanta wannan

Yadda aka kamo wasu mutum 5 da suka yunkurin siyar da jariri mai kwanaki 8 a Kano

An ba Tinubu shawari

A wani labarin, Wasiu Olawale Sadare, kakakin jam’iyyar APC na jihar Oyo, ya bayyana abubuwa biyar da ya kamata shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi domin kare tattalin arzikin Najeriya daga kara durkushewa.

Jigon na jam’iyyar APC ya bayyana cewa idan aka dauki matakan, za a samu mafita a gwamnatin Tinubu wajen biyan bukatun kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da TUC tare da dakile shirin yajin aikin da suke shirin yi.

Idan baku manta ba, kungiyoyin biyu sun shirya shiga yajin aiki, wanda suka farawa daga ranar Talata, 3 ga Oktoba, 2023, duk da rokon da gwamnati ta yi na su dakata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.