Babban Dalilin da Yasa Najeriya Ta Gaza Gano Hanyoyin Warware Matsalolinta, Inji Fasto Oyedepo
- Babban fasto kuma shugaban jami'a ya bayyana kadan daga matsalolin da Najeriya ke fuskanta a yanzu
- Ya nemi jami'o'in kasar nan su zama masu maida hankali ga mafita ga matsalolin da al'umma ke ciki
- Ya kuma shawarci gwamnati ta kasance mai nemo mafita tare da aiki da hakan a wa'adin mulki
Shugaban Jami’ar Covenant da ke Ota, Dokta David Oyedepo, ya ce Najeriya ba ta lalubo hanyoyin magance matsalolinta ba saboda jama’a ba su shirya yin abin da ya dace ba, PM News ta ruwaito.
Oyedepo, wanda kuma kuma babban fasto ne Living Faith Churches Worldwide, ya kuma shawarcu jami’o’in Najeriya shawara da su yi kokarin kara kaimi wajen yin bincike domin magance matsalolin al’umma.
Abin da ya kamata jami'o'i suke yi
A cewar Oyedepo, akwai bukatar jami’o’i su ci gaba da gudanar da bincike mai inganci wanda zai kawo wadatar abinci, inganta lafiya, inganta harkar noma da muhalli ga kowa a kasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kalamansa, cewa ya yi:
“Kowace matsala da gani tana da mafita. Amma idan babu mai warware matsala, irin wadannan matsalolin sai su zama abin da ba a za a iya warwarewa ba.
"Muddin muka ci gaba da kasancewa a tsarin kowa ta kansa, za mu ci gaba da komawa baya."
Matsalolin al'umma a Najeriya
Shugaban jami;ar ya bayyana jami’o’i a matsayin wuraren da ya kamata ake samun hanyoyin magance matsalolin al’umma da kuma kara shajja'a kimar bil’adama, rahoton Peoples Gazette.
Ya ambaci wasu daga matsalolin al’umma da suka hada da bukatuwa ga wadataccen abinci, ingancin noma, kula da lafiya, muhalli, haihuwa da kulawa da dai sauransu.
Allah na fushi damu a Najeriya, inji jigon siyasa
A wani labarin na daban, tsohuwar jigon siyasa a Najeriya ta bayyana kadan daga tushen matsalolin Najeriya da dalilin da yasa aka gaza nemo mafita.
A cewar Alhaja Sinatu Ojikutu, Allah na fushi da Najeriya shi yasa komai ke tafiya a bai-bai a madadin a ci gaba.
Tun bayan samun 'yancin kai a Najeriya ake fuskantar matsalolin da har yanzu ba a samu mafita ba.
Asali: Legit.ng