Yan Bindiga Sun Kona Gidan Wani Dan Majalisa a Jihar Imo

Yan Bindiga Sun Kona Gidan Wani Dan Majalisa a Jihar Imo

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun cinnawa gidan wani babban ɗan majalisar wakilai wuta a jihar Imo
  • Ƴan bindigan sun cinnawa gidan ɗan majalisar wakilan wanda ke wakiltar mazaɓun Orlu/Oru ta Gabas/Orsu wuta bayan sun kai wani farmaki
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta bayyana cewa tuni ta fara bincike kan lamarin

Jihar Imo - Ƴan bindiga sun ƙona gidan dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Orlu/Oru ta gabas/Orsu na jihar Imo a majalisar wakilai, Canice Nwachukwu (wanda aka fi sani da Omeogo).

Jaridar The Punch ta tattaro cewa an ƙona gidan ɗan siyasar ne da safiyar ranar Alhamis, sa’o’i kadan kafin a fara taron kwanaki biyu kan tattalin arziƙi da tsaron yankin Kudu maso Gabas, a birnin Owerri, wanda gwamnonin yankin biyar suka halarta.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Ta Kira Zaman Gaggawa da NLC da TUC a Abuja, Bayanai Sun Fito

Yan bindiga sun kona gidan dan majalisa a Imo
Gidan dan majalisar da yan bindigan suka kona Hoto: Punchng.com
Asali: UGC

Yadda ƴan bindigan suka kona gida

Majijoyi sun bayyana cewa ɗan siyasar baya gida lokacin da wadanda ake zargin suka aikata ƙone-ƙonen bayan sun isa gidan ɗan majalisar tarayyar da ke a ƙauyen Abara cikin gundumar Amanator Okporo a ƙaramar hukumar Orlu ta jihar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mutanen sun zo ne da abubuwan fashewa da man fetur. Kafin cinnawa gidan wuta, sun yi awon gaba da wasu kadarori. Haka kuma sun yi faifan bidiyo na gidan da ma'aikatan gida."
"Lokacin da suke yin faifan bidiyon, sun yi barazanar shirya wasu ta'addancin. Sun zo da bindigogi, da abubuwa masu fashewa kamar bama-bamai da aka yi a cikin gida. Ma’aikatan sun yi sa’a sun tsere kafin su banka wa ginin wuta."

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Henry Okoye, ya ce sun fara gudanar da bincike kan lamarin, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Jerin Fastocin Da Suka Yi Hasashen Za a Cafke Peter Obi a Watan Satumba

Yan Sanda Sun Cafke Masu Garkuwa Da Mutane

A wani labarin na daban, jami'an ƴan sanda a jihar Benue da ke yankin Arewa ta Tsakiya sun samu nasarar cafke wasu miyagun masu garkuwa da mutane da suka addabi al'ummar jihar.

Jami'an ƴan sandan sun cafke miyagun su huɗu waɗanda ake zargi da aikata laifukan na satar mutane domin amsar kuɗin fansa, sannan suka kubutar da mutum shida da suka yi garkuwa da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel