Masu Zanga-Zanga Ba Su Garkame Minista a Ofishinsa Ba, Ma’aikatar Ayyuka Ta Magantu

Masu Zanga-Zanga Ba Su Garkame Minista a Ofishinsa Ba, Ma’aikatar Ayyuka Ta Magantu

  • An yada labarin yadda aka garkame ministan ayyuka na Najeriya a ofishinsa saboda wasu dalilai
  • Sai dai, rahoton da ke fitowa daga majiya ya bayyana cewa, ba haka abin ya faru ba, ba a garkame ministan ba
  • Tun bayan janye tallafin man fetur a Najeriya ma'aikata ke ci gaba da kuka da yanayin da suka tsinci kansu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Ma’aikatar ayyuka ta tarayya ta ce ba a kulle ministanta David Umahi a ofishinsa ba, ba a kuma hana shi shiga ba, sabanin rade-radin da ake ta yadawa a wasu kafafen yada labarai.

A tun farko, ma’aikatar ta bayyana cewa a wani bangare na kokarin da ministan ke yi na ganin ma’aikatan sun nuna da’a a ayyukansu, ya ba da umarnin a fara aiki daga karfe 9 na safe daga ranar Litinin zuwa Juma’a.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Masu Zanga-Zanga Sun Kulle Ministan Tinubu a Ofis, Bayanai Sun Fito

Hakazalika, ministan ya umarci a koma tashi daga aiki a dukkan nau'ikan ma’aikatansa da misalin karfe 4 na yamma, The Nation ta ruwaito.

Ba a garkame minista Umahi a ofis ba, inji ma'aikatar ayyuka
Batun garkame minista a ofishinsa jiya Alhamis | Hoto: @ABATofficial, @DaveUmahi
Asali: Twitter

Yadda ma'aikatan suka fusata

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa wasu jami’an ma’aikatar sun nuna bacin rai tare da yin zanga-zanga kan umarnin da ministan ya bayar, inda suka kulle kofar shiga ma’aikatar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An tattaro cewa Umahi ya bada umarnin a kulle kofar shiga ma’aikatar a jiya domin sanin ma’aikatan da suka makara da zuwa aiki.

Ma’aikatan sun koka da cewa duk da cewa matakin da ministan ya dauka ba daidai bane, inda suka ce an dauki matakin ba tare da sanar dasu ba.

Halin da ma'aikata ke ciki

Wani jami’in ma’aikata ya bayyana cewa, baya ga tsadar kudin sufuri, shi da sauran ma’aikatan da ke zaune a wurare nesa da sakatariyar gwamnatin tarayya sukan samu jinkirin samun abin hawa.

Kara karanta wannan

Rundunar Tsaro Ta Bayyana Dalili 1 Tak Da Ke Hana Su Kawo Karshen Rashin Tsaro, Ta Yi Bayani

Tun bayan cire tallafin man fetur ma'aikata a Najeriya ke kuka kan yadda tsadar abin hawa da kayan abinci ke shafar rayuwarsu ta yau da kullum, rahoton Vanguard.

Wasu daga cikin wuraren da suke rayuwa a cewarsa, sun hada da: Keffi, Kwali, Bwari, Kaduna road, Gwagwalada, da dai sauransu.

Wike ya kori ma'aikata a FCTA

A wani labarin, Nyesom Wike ya sake zuwa da batun da zai jawo cece-kuce a Najeriya, ya yi kakkaba tare da korar wasu manyan ma'aikata a hukumar kula da lamurran babban birnin tarayya Abuja.

Raahoton da muke samu ya bayyana cewa, Wike ya yi wannan korar ne a ranar Laraba 27 ga watan Satumba mai karewa na wannan shekarar.

Ya zuwa yanzu, rahoton da kuma sanarwar da ministan ya fitar bai bayyana gaskiyar dalilin da yasa aka yi wannan dakatarwa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.