Masu Zanga-Zanga Sun Kulle Ministan Ayyuka a Ofishinsa
- Ministan ayyuka na gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya samu saɓani da ma'aikatan da ke aiki a ma'aikatarsa
- Ma'aikatan sun gudanar da zanga-zanga domin nuna adawa kan yadda Dave Umahi yake tsaurara musu a wajen aiki
- Ma'aikatan sun kulle ministan a ofishinsa. da hana shiga da fita cikin ma'aikatar bayan wasu daga cikinsu sun zo a makare ya hana su shiga
FCT, Abuja - Masu zanga-zanga sun kulle ministan ayyuka, Dave Umahi a cikin ofishinsa da ke ma'aikatar ayyuka a birnin tarayya Abuja.
Ma'aikatan masu gudanar da zanga-zangar sun garƙame ministan ne a ofishinsa bayan sun zarge shi da cika tsaurarawa., cewar rahoton AIT.
Rahotanni sun ce ministan ya hana ma'aikatan da suka zo wurin aiki a makare samun damar shiga cikin ma'aikatar, rahoton Leadership ya tabbatar.
Rikici Ya Kunno Kai, Gwamnan PDP Ya Tona Asiri, Ya Ce Ko Kwandala Bai Gani Ba a Baitul Malin Jihar Arewa
Meyasa ma'aikatan suka kulle Umahi a ofis?
Ƙungiyoyin ma'aikatan waɗanda suka haɗa da ma'aikatan ma'aikatar ayyuka da na ma'aikatar gidaje, sun yanke shawarar kulle ma'aikatar, inda suka kulle duk wata ƙofar shiga da fita daga ma'aikatar tare da hana ministan ya fita daga ofishinsa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sun kuma yi iƙirarin cewa ya hana injiniyoyi da daraktoci yin aikinsu, kuma tun bayan nada shi ya ke karya ƙa’idojin aikin gwamnati, ta hanyar kawo masu ba da shawara don tafiyar da harkokin ma'aikatar.
Wani jami’in kungiyar, Williams Kudi, ya bayyana cewa ministan ya ƙi ba su dama su bayyana masa ƙorafen-ƙorafen da suke da su.
Ƙoƙarin jin ta bakin ministan da hadimansa ya ci tura, domin ba a samu layukan wayoyinsu ba lokacin da aka kira.
Masu Zanga-Zanga Sun Karya Kofar Majalisa
A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa masu gudanar da zanga-zanga domin adawa da matakan da Shugaba Timubu ke ɗauƙa domin farfaɗo da tattalin arziƙi, sun kutsa cikin harabar majalisar dattawa.
Gwamnan Zamfara Ya Fusata Kan Satar Daliban Jami'ar Gwamnatin Tarayya, Ya Fadi Muhimmin Kokarin Da Yake Yi
Masu gudanar da zanga-zangar sun samu damar kutsawa cikin harabar majalksae ne bayan karairaya ƙofar shiga cikon majalisar. Masu zanga-zangar dai sun karya ƙofar ne bayan jami'an tsaro sun hanasu shiga cikin majalisar.
Asali: Legit.ng