Tsohon Shugaban Hukumar FIRS, Nami Ya Kwashe Naira Biliyan 11 Kwanaki Biyu Bayan Barin Ofis

Tsohon Shugaban Hukumar FIRS, Nami Ya Kwashe Naira Biliyan 11 Kwanaki Biyu Bayan Barin Ofis

  • Ana zargin tsohon shugaban hukumar FIRS da hamdame makudan kudade kwanaki biyu bayan barin ofis
  • Muhammad Nami kamar yadda aka ruwaito ya amince da Naira biliyan 11 don tura su zuwa wasu wurare
  • Wannan na zuwa ne kwanaki biyu bayan Shugaba Tinubu ya nada Zacchaeus Adedeji don maye gurbinshi

FCT, Abuja – Tsohon shugaban hukumar FIRS, Muhammad Nani ya amince da makudan kudade ga ‘yan kwangiya bayan an kore shi daga mukaminsa.

Nami ya salwantar da kudade har Naira biliyan shida jim kadan bayan barin ofis wanda ya tura su ga wasu ‘yan kwangila.

Ana zargin tsohon shugaban FIRS, Nami da badakalar N11bn
Ana zargin Muhammad Nami da handame N11bn bayan korarshi a hukumar FIRS. Hoto: Muhammad Nami.
Asali: Twitter

Meye ake zargin Nami kan kudaden FIRS?

TheCable ta tattaro cewa Shugaba Tinubu ya nada Zacchaeus Adedeji don maye gurbin Nami a matsayin shugaban hukumar FIRS.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Hukumar INEC Ta Fallasa Matsalar da Ta Hango Gabanin Zaben Gwamna a Jihohi 2

Ana zargin Nami ya kwashe kudaden ne kwanaki biyu bayan an kore shi a matsayin shugaban hukumar a ranar 14 ga watan Satumba.

Wata majiya ta tabbatar cewa Nami ya bukaci ma’akatan bangaren kudi da bincike su yi aiki ranar Asabar da Lahadi don cire kudaden.

Wannan na zuwa bayan dukkan takardun da ke da alaka da kudaden an dauke su zuwa gidansa inda aka sauya musu kwanan wata.

Har ila yau, Nami ya kuma ya tura Naira biliyan biyar daga asusun FIRS zuwa asusun Hukumar Haraji (JTB).

Yadda Nami ya kwashe kudaden FIRS

Rahotanni sun tabbatar da cewa daraktan bangarorin da su ka yi aikin ya gargadi Nami kan matsalar hakan a gaba amma ya ki ji.

Yayin da Nami ya bai wa daraktan tabbacin cewa babu abin da zai faru inda ya ce sabon shugaban ba zai fahimci komai ba, TheNewsGuru ta tattaro.

Wani dan uwan Nami wanda shi ma mataimakin manaja ne a hukumar mai suna Jibrin Jibrin ya tabbatarwa wasu daga cikin ma’aikata cewa wannan kudaden ba za su ta da kura ba.

Kara karanta wannan

Shugabar Karamar Hukumar da Ya Zargi Gwamnan APC da Wawure Kuɗi Ya Shiga Sabuwar Matsala

An tabbatar cewa Nami ya tsallake zuwa kasar ketare bayan amincewa da wannan kudaden a ranar 16 ga watan Satumba.

Nami ya yi martani bayan Tinubu ya kore shi a FIRS

A wani labarin, tsohon shugaban hukumar FIRS, Muhammad Nami ya yi martani a karon farko kan korarshi da Tinubu ya yi.

Shugaba Tinubu ya kori Nami a ranar 14 ga watan Satumba inda ya nada Zacchaeus Adedeji a matsayin shugaban hukumar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.