“Ina Mutunta Kudi”: Kyakkyawar Mata Ta Nunawa Duniya Mijinta Dan Dattijo a Bidiyo
- Wata matashiyar mata ta kasance cikin farin ciki yayin da ta dauki bidiyonta tare da mijinta dan dattijo, wanda ke cike da kamala
- Kyakkyawar matar ta nunawa mijin nata so da kauna tsantsa yayin da take taka rawa, inda shi kuma yake zaune waje guda a bidiyon
- Yan Najeriya da dama da suka ga bidiyon sun bayyana ra'ayoyinsu, yayin da mutane da dama suka taya ta addu'an samun farin ciki a gidan aurenta
Wata matashiya yar Najeriya wacce ta aure wani dattijo ta haddasa cece-kuce tsakanin yan Najeriya yayin da ta baje kolin mijinta.
Matashiyar, @asmawu.hamisu, ta kira dattijon da "rayuwata" sannan ta rike hannunsa a kan teburin cin abinci yayin da suke bidiyon a TikTok.
Matashiya da dattijon mijinta
Alamu sun nuna mijin yana da sanyin hali yayin da matashiyar take ta matso kyau a gaban kamara. Binciken da aka gudanar a shafinta na TikTok ya nuna tana jin dadin rayuwa tare da murza kudi yadda take so.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cikin wani bidiyon, matashiyar ta kasance sanye da doguwar riga fara irin na amare a ranar aurensu, inda shi kuma angon ya sanya farin yadi dinkin babbar riga.
Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a a kasa:
Ekuaamoakowaa ya ce:
"Sashin bincikena na cewa ivy ifeoma da mijinta."
Cee jay ta ce:
"Ke kadai ce...regina daniel da ivy ifeoma ne kawai za su iya ba ni shawara a duniyar nan."
Yasmin Trunesh Hussein Ndiema ta ce:
"Duk mun yarda cewa imma dai hanyar Regina Daniels ko hanyar Kanayo .O Kanayo."
HAWERO ya ce:
"Idan dai har kina cikin farin chomi."
Jordan kudus ta ce:
"Ina girmama ka kudi."
@preshchuks ta ce:
"Ke da Regina ne kawai za ku iya ba ni shawara a shekarar nan."
Chachaluv ta ce:
"Ki bi kudi, soyayya za ta biyo baya na fahimce ki yar'uwa."
Matashiya Ta Girka Abinci Iri-Iri, Ta Ce Kudinsu Miliyan 3.2
A wani labari na daban, wata yar Najeriya mai girke-girke ta haddasa cece-kuce a tsakanin mutane bayan ta wallafa bidiyon abinciki da ya kai sama da naira miliyan 3.
Mai girkin (@hotmbycheft) ta sanar da cewar ranar zagayowar haihuwarta ne yayin da ta jefa abinciki a kan teburinta da taimakon hadimanta.
Asali: Legit.ng