Dangote Ya Yi Magana Kan Batun Karya Farashin Buhun Siminti a Najeriya

Dangote Ya Yi Magana Kan Batun Karya Farashin Buhun Siminti a Najeriya

  • Kamfanin Ɗangote ya bayyana gaskiya kan rahoton da ke yawo cewa ya karya farashin buhun siminti daga N5,000 zuwa N2,500
  • Rahoton ya yi ikirarin cewa sabon farashin buhun simintin Ɗangote zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Octoba, 2023
  • Legit Hausa ta tuntuɓi kamfanin Ɗangote domin tabbatar da batun sabon farashin buhun simintin wanda zai fara nan da 'yan kwanaki

Kamfanin Ɗangote Group, uwa ga kamfanin simintin Ɗangote ya musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa ya karya farashin buhun siminti da kashi 50.9% daga ranar 1 ga watan Oktoba.

A wani saƙo da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta daban-daban, wanda ya haɗa da Whatsapp, an ce wai Ɗangote na shirin rage farashin siminti a faɗin Najeriya.

Dangote ya musanta rahoton karya farashin siminti.
Dangate Ya Yi Magana Kan Batun Karya Farashin Buhun Siminti a Najeriya Hoto: Tom Saater
Asali: Getty Images

Saƙon da mutane ke ta turawa a shafukan sada zumuntan ya ce:

Kara karanta wannan

Kungiyoyin Kwadago NLC da TUC Sun Ayyana Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani a Najeriya, Sun Faɗi Rana

"Ɗangote ya karya farashin siminti daga N5,500 zuwa 2,700 kan kowane buhu ɗaya. Aliko Ɗangote da kansa ya sanar da sabon farashin wanda ya rage aƙalla kashi 50%."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Sabon farashin zai shiga kasuwa daga ranar 1 ga watan Oktoba, 2023, zai sauko daga N5,000 zuwa N2,700."

Ɗangote ya maida martani

Da yake jawabi ga wakilin jaridar Legit Hausa, jami'in hulɗa da jama'an na rukunin masana'antun Ɗangote, Anthony Chiejina, ya bayyana rahoton da labarin ƙanzon kurege.

Ya bayyana cewa rahoton da ake yaɗawa na karya farashin simintin Ɗangote a faɗin Najeriya ba gaskiya bane.

Yadda BUA ke shirin rage farashin siminti

Jita-jitar rage farashin simintin Ɗangote na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban rukunin kamfanonin BUA Group, Abdul-Samad Rabiu ya fitar da sanarwa.

Rabiu ya bayyana cewa kamfaninsa ya kudiri aniyar karya farashin buhun siminti a Najeriya daga N5,500 da ake siyarwa a yanzu zuwa tsakanin N3,000 zuwa N3,500.

Kara karanta wannan

Gobara Ta Laƙume Takardun Ƙarar Zaben Shugaban Ƙasa a Kotun Ƙoli? Gaskiya Ta Bayyana

Ya faɗi haka ne jim kaɗan bayan ganawa da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a fadar shugaban ƙasa ranar Jumu'a 15, ga watan Satumba, 2023.

Wani ɗan kasuwar siminti, Alhaji Lawal Mai Siminti, ya faɗa wa wakilin Legit Hausa cewa dama tunda ya ji labarin a bakin mutane yake tantama a kai.

Ya ce:

"Na ji mutane na ta magana kan rage farashin siminti, wasu kaji suna gode wa Ɗangote, amma da na kira waya inda ake turo mana da kaya aka ce mun ba gaskiya bane."
"A yanzu kayan dake wurina duk buhu ɗaya muna bada shi a kan N4,800 ne, to amma yanayin kasuwa, wani lokacin sai kaje siyo wa daga sama a ce maka ya tashi ko ya sauka."

Gwamnatin Bola Tinubu Ta Bayyana Ranar Hutun Maulidi a Najeriya

A wani rahoton kuma Gwamnatin tarayya karkashin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta bada hutun kwana ɗaya domin bukuwawan Maulidi na shekarar 1445/2023.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi- Yan Daba Sun Lalata Ofishin Jam'iyyar APC, Bayanai Sun Fito

A wata sanarwa, Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ayyana ranar Laraba, 27 ga watan Satumba a matsayin ranar hutun Maulidin Nabiy.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262