Gobarar Kotun Koli Ba Ta Kona Takardun Karar Zaben Shugaban Kasa Ba, Kakaki
- Kotun ƙolin Najeriya ta bayyana cewa gobarar da ta faru bata shafi ƙarar zaben shugaban ƙasa ba kamar yadda ake yaɗawa
- Mai magana da yawun Ƙotun, Dakta Festus Akande, ya ce kayayyakin da wutar ta cinye za a iya maida su saboda akwai ɗakin karatu na Intanet
- A halin yanzu hukumar 'yan sanda ta kaddamar da bincike don gano dalilin tashin gobara a Kotu lamba ɗaya a Najeriya
FCT Abuja - Daraktan yaɗa labarai da tattara bayanai na Kotun ƙolin Najeriya, Dakta Festus Akande, ya yi ƙarin haske kan gobarar da ta faru a wani sashin ginin Kotun.
Mista Akande, ya ce wutar da ta tashi a Kotun ƙoli ba ta taɓa komai ba da ya shafi kotun sauraron ƙararraƙin zaben shugaban ƙasa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Idan baku manta ba mun kawo muku rahoton yadda Gobara ta babbake wasu sassan kotun koli da ke babban birnin tarayya a ranar Litinin, 25 ga watan Satumba, 2023.
Sai dai tuni jami'an hukumar kashe gobara da dakarun 'yan sandan Najeriya suka shawo kan lamarin bayan ƙashe wutar baki ɗaya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shin da gaske gobarar ta cinye takardun ƙarar zaben shugaban ƙasa?
Da yake hira da 'yan jarida kan ibtila'in da ya auku, Mista Akande ya ce ɓangare ɗaya tak na Kotun Ƙolin gobarar ta shafa, kuma an kashe ta a kan lokaci.
Kakakin Kotun Ƙolin ya ce:
"Abubuwan da suka ƙone a ɓangaren da wutar ta yi ɓarna su ne littattafai, kayan rubutu, da sauran kayan aikin kwamfuta. Ana iya maye gurbin littattafan saboda muna da ɗakin karatu na e-library."
"Muna da kwafin litattafan a na'ura mai ƙwakwalwa kuma akwai litattafan a kasuwa, za a iya siya a kai sashin da lamarin ya shafa. Saboda haka babu abin da ya faru da takardun ƙarar zaben shugaban ƙasa kamar yadda ake yaɗawa."
Gwamnan PDP a Arewa Ya Maida Martani Bayan Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Da Ya Samu a 2023
"Irin waɗan nan batutuwa kamar na zaɓen shugaban ƙasa ba a aje su a ɓangaren da wutar ta yi ɓarna a harabar Kotun kolin."
A halin yanzu, rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta fara gudanar da bincike kan lamarin, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar PDP Ya Gamu da Mummunan Hatsari
A wani rahoton kuma Kakakin majalisar dokokin jihar Osun ya tsallake rijiya da baya yayin da haɗarin mota ya rutsa da ayarinsa a Osogbo ranar Lahadi.
Wata majiya ta bayyana cewa kakakin ya sha babu abinda ya same shi amma wasu jami'an tsaro huɗu sun samu raunuka.
Asali: Legit.ng